Kotu ta taka wa EFCC burkin gaggawar kamo Diezani daga Landan

0

Tsohuwar Ministar Fetur a zamanin mulkin Goodluck Jonathan, Diezani Allison-Maduekwe, ta samu daga kafa daga Babbar Kotun Tarayyar Najeriya cewa EFCC su dakatar da neman kotu ta ba hukumar sammacin kamo ta da karfin tsiya.

Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta ce EFCC ta nemi kotun ta bayar da sammacin ta bahaguwar hanyar, da tilas kotin ta ta hana sammacin, ta ce EFCC ta baro shiri tun a gida, sai ta koma ta sake kimtsawa ta dawo kotun tukunna.

EFCC ta nemi Mai Shari’a Ijeoma ta bada sammacin kamo Deizani ko da tsiya, sai da kuma Mai Shari’ar ta maida EFCC kan hanya, ta ce ai a baya an bada takardar neman bayyana kotu.

“Don haka kotu ba za ta bada wani sammaci ba, har sai EFCC ta bai wa wannan kotu shaida cewa wancan sammaci na baya ba shi da karfin kawo wadda ake tuhuma din a kotu.

“A iya sani na, kotu ta bada takarda ga EFCC a baya, a karkashin Sashin Doka na ACJA, ta 831. Don haka sai dai EFCC ta koma ta nemi hadin kai da Ministan Shari’a domin a gabatar da wadda ake tuhuma a kotu. Tunda dai an tabbatar ta na Landan.”

Idan ba a manta ba, dakataccen Shugaban EFCC Ibrshim Magu ya yi kokarin hada kai da ‘Yan Sandan Kasa-da-kasa (INTERPOL) cewa duk inda aka Deizani a kamo ta, a taso keyar ta zuwa Najeriya.

Amma da abin ya gagara, Magu ya yi zargin Birtaniya na yi wa shirin maido Deizani Najeriya kafar-ungulu.

Tsohuwar Ministar Fetur din dai ta arce zuwa Ingila tun bayan faduwa zaben da gwamnatin Jonathan ta yi a 2015.

An maka ta kotu, inda daga can Birtaniya din ta rika karyata zarge-zargen da mahukuntan Najeriya su ka yi mata.

A can din ma, gwamnatin kasar na Tuhumar ta ne da zargin karkatar da kudade.

Babbar Kotun Najeriya dai ta shaida wa EFCC ta sake shirin kokarin maido da Deizani Najeriya a kan ka’ida.

Za a koma Kotu cikin Disamba.

Share.

game da Author