KORONA: Yaran Makaranta 181 da malamansu sun kamu da Korona a wani makaranta a Legas

0

Akalla dalibai da malaman su 181 ne aka tabbatr sun kamu da Korona da wani makaranta mai zaman kansa a Legas.

Ma’aikatar kiwon Lafiya ta jihar Legas ta sanar cewa yaran makaranta 181 da wasu malaman su sun kamu da Korona a wani makarantar Kwana dake Lekki, Jihar Legas.

Kwamishinan Lafiya na jihar Akin Abayomi, ya shaida cewa bincike da aka gudanar ne ya sa aka gano wadanda suka kamu da cutar.

” Wata daliba ‘yar ajin SSII ce ta fara rashin Lafiya, da aka kaita asibitin makarantar, a nan ne aka gano ta Kamu da Korona. Da aka yi wa daliban makarantar gwaji sai aka gano yara 181 duk sun kamu da wasu daga cikin malaman su.

” Sai dai cutar bata kwantar da su ba dukkan su. Mun shawar ce su da su cigaba da zama a makarantar kada kuma su koma gida su yada cutar, sannan kuma mun tura malaman lafiya su ci gaba da samar da kula a wurin da kewaye.”

Share.

game da Author