KORONA: Wuraren holewa da gidajen Casu za su cigaba da zama a garƙame har zuwa wani lokaci – PTF

0

A ranar Alhamis ne kwamitin Shugaban kan Korona PTF ta shaida cewa baza a bude wuraren shakatawa da kulob ba saboda akai yiwuwar idan a ka bude su za a samu karuwar yaduwar Korona a kasar nan.

Kodinatan kwamitin Sani Aliyu ya sanar da haka a ganawa da kwamitin ta yi da manema labarai a Abuja.

“Ba wai kwamitin bata so a bude ire-iren wadannan wurare bane, tsarin su bai yi kama da inda za a kiyaye dokokin Korona ba.

“A dalilin haka muke bai wa masu zuwa holewa a wurare irin haka da su kara hakuri har sai gwamnati ta gamsu da tsarin wuraren kafin ta bude su.

Shima sakataren gwamnati tarayya kuma shugaban kwamitin PTF Boss Mustapha ya tabbatar da haka yana mai cewa a wurare irin haka babu yadda za a yi a iya kiyaye dokokin Korona.

Mustapha ya ce Idan aka kara hakuri zuwa dan wani lokaci kadan komai zai koma yadda ya ke a da.

Ya ce daukan wannan matakin ya Zama dole ganin cewa babu tabbacin samun maganin rigakafin cutar a kasar nan nan da watanni shida masu zuwa.

Sakamakon binciken NCDC ya nuna cewa Najeriya ta fara samun nasara wajen rage yaduwar cutar korona a kasar Nan.

Binciken ya nuna cewa makonni hudu da Suka gabata adadin yawan mutanen dake kamuwa da cutar basu dara 300.

Sai dai duk da nasarorin da ake samu kwamitin PTF ta koka cewa jihohi 26 basu yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar nan.

Hakan kuwa na kara ingiza mutane wajen rashin amincewar da cutar a kasar nan.

A dalilin haka kwamitin ya yi Kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye dokokin Korona a ko-ina suke.

Zuwa yanzu mutum 60,982 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 52,194 sun warke, 1,116 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,672 ke dauke da cutar a Najeriya.

Sannan tun bullowar cutar an yi wa mutum 567,857 gwajin cutar.

Share.

game da Author