KORONA: Mutum miliyan 35 suka kamu a duniya, miliyan 1.5 a Afrika

0

Alkaluman sakamako rahoton ‘Wordometer’ na yawan wadanda suka kamu da Korona a duniya tun barkewar annobar ya nuna akalla mutum miliyan 35,139,699, suka kamu, a Nahiyar Afrika kuma mutum miliyan 1.5.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce adadin yawan mutanen dake dauke da cutar a yanzu ya ninka yawan mutanen da kan kamu da cutar mura sau biyar a shekara a duniya.

Zuwa yanzu kasashen US, India da Brazil ne suka fi fama da cutar a duniya.

A dalilin haka ne WHO ta yi gargaddin cewa cutar za ta fi haka yaduwa nan gaba Idan ba a yi hankali ba.

Bayan haka rahotan ya nuna cewa cutar ta yadu zuwa sama da rabin kasashen Turai domin a cikin makonni biyu da suka gabata yankin ta samu karin kashi 10 a yawan mutanen da suka kamu da cutar.

Duk da haka kasashen U.S., India da wasu kasashen Kudu maso Amurka na kan gaba wajen jerin kasashen da cutar ta yi wa katutu a duniya.

An sallami mutum 26,128,410 a duniya.

Korona ta kashe mutum 1,038,027 a duniya.

Sakamakon rahoton ‘Worldometers’ ya nuna cewa cutar korona ta yi ajalin mutum 1,038,027 a duniya.

Kasar Amurka ce kasar da ta fi yawan mutanen da suka mutu a dalilin kamuwa da kwayoyin cutar.

Kasashen Mexico, Peru, Colombia, Chile da Ecuador na daga cikin kasashen da mutane suka fi mutuwa a yankin kudancin Amurka.

Nahiyar Afrika

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC ta bayyana cewa cutar korona ta kashe mutum 36,000 a Afrika.

Zuwa yanzu mutum 1,506,185 ne suka kamu da cutar a Afrika.

An sallami mutum 1,127,034 daga cikin mutum 1,506,185 da suka kamu da cutar.

Cutar ta yadu zuwa Kasashe 54 dake Nahiyar Afrika.

Gwamnatocin Nahiyar Afrika na kokarin ganin yadda za su iya farfado da tattalin arzikin yankin da cutar korona ta gurgunta.

Najeriya

A ranar Lahadi 4 ga watan Oktoba mutum 58 be suka kamu da cutar inda haka ya nuna mafi kankantan yawan mutanen da Suka kamu da cutar tun bayan bullowar cutar a Najeriya.

Mutum 59,345 suka kamu da cutar, 50,768 sun warke, 1,113 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,464 ke dauke da cutar a Najeriya.

Share.

game da Author