Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 170 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –106, FCT-25, Oyo-14, Edo-7, Kaduna-7, Ogun-4
Bauchi-2, Benue-2, Kano-1, Osun-1 da Rivers-1.
Yanzu mutum 62,691 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 58,430 sun warke, 1,144 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,117 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 21,212, FCT –6,053, Oyo – 3,433, Edo –2,664, Delta –1,814, Rivers 2,810, Kano –1,747, Ogun –2,031, Kaduna –2,648, Katsina -952, Ondo –1,666, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 713, Ebonyi –1,049, Filato -3,630, Enugu – 1,314, Abia – 898, Imo –616, Jigawa – 325, Kwara – 1,069, Bayelsa – 412, Nasarawa – 482, Osun –926, Sokoto – 165, Niger – 274, Akwa Ibom – 295, Benue – 493, Adamawa – 252, Anambra – 277, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 332, Taraba- 146, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
An samu ragowar yaduwar cutar yayin da gwamnati ta dage wajen tsananta yin gwaji
Sakamakon bincike ya nuna cewa yaduwar cutar korona ya ragu zuwa Kashi 50 bisa a kasar nan.
Hakan ya faru ne a dalilin zage damtse da gwamnati ta yi wajen tsananta yin gwajin cutar.
Bisa ga sakamakon gwajin da hukumar NCDC ta fitar ya nuna cewa an samu jimlar mutum 623 da suka kama cutar tsakanin ranar 18 zuwa 24 ga Oktoba.
A wancan makon da ya gabata mutum 1,204 suka kama cutar a kasar nan.
Tun da cutar ta bullo a watan Fabrairu mutum 620,758 be aka Yi wa gwajin cutar a Najeriya.
Hukumar NCDC ta ce Najeriya ta samu ragowa a yawan mutanen dake warkewa daga cutar da yawan dake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar.
Discussion about this post