KORONA: Mutum 164 suka kamu ranar Litini, Yanzu mutum 60,430 suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 164 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –64, FCT-26, Enugu-20, Kaduna-11, Oyo-11, Plateau-8, Ondo-7, Anambra-4, Nasarawa-3, Osun-3, Ebonyi-2, Imo-2, Benue-1, Katsina-1 da Ogun-1

Yanzu mutum 60,430 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 51,943 sun warke, 1,115 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,372 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 20,086, FCT –5,832, Oyo – 3,315, Edo –2,636, Delta –1,803, Rivers 2,661, Kano –1,740, Ogun – 1,940, Kaduna –2,519, Katsina -896, Ondo –1,650, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 710, Ebonyi –1,044, Filato -3,545, Enugu – 1,309, Abia – 898, Imo – 585 , Jigawa – 325, Kwara – 1,050, Bayelsa – 403, Nasarawa – 472, Osun –906, Sokoto – 162, Niger – 261, Akwa Ibom – 295, Benue – 483, Adamawa – 254, Anambra – 250, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 323, Taraba- 108, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.

Idan ba a manta ba, Ministan harkokin mata da ci gaban al’umma Pauline Tallen ta bayyana cewa mata ne Korona ta fi yi wa illa a Najeriya fiye da maza.

Pauline ta fadi haka ne a taron tattauna daidaita jinsin maza ta mata domin a samu damawa da mata a harkokin gwamnati da ci gaban al’umman kasar nan.

Ta ce a lokacin da aka saka dokar Kulle, mata ne suka fi fadawa cikin kuncin rayuwa. Tace sanin kowa ne cewa mata da yawa sukan dan yi kasuwanci ne na yau da kullum. Rashin fita da ba sa iya yi ya talauta su da yawa.

Share.

game da Author