Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 153 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 81, Rivers-21, FCT-11, Ogun-8, Kaduna-7, Oyo-6, Akwa Ibom-5, Osun-3, Katsina-3, Edo-2, Ebonyi-2, Nasarawa-2, Filato-1 da Kano-1.
Yanzu mutum 59,001 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 50,452 sun warke, 1,112 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,378 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 19,542, FCT –5,720, Oyo – 3,267, Edo –2,628, Delta –1,802, Rivers 2,453, Kano –1,738, Ogun – 1,858, Kaduna –2,426, Katsina -864, Ondo –1,631, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 699, Ebonyi –1,042, Filato -3,451, Enugu – 1,289, Abia – 895, Imo – 572, Jigawa – 325, Kwara – 1,036, Bayelsa – 399, Nasarawa – 452, Osun –842, Sokoto – 162, Niger – 259, Akwa Ibom – 293, Benue – 481, Adamawa – 248, Anambra – 237, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 76, Ekiti – 321, Taraba- 102, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Masana kimiya za su tabbatar maganin Korona da za a fitar ya tsallake gwajin tabbatar da ingancin sa.
Masana kimiya dake aiki da kamfanonin sarrafa magunguna guda Tara sun yi alkawarin hadawa da samar da maganin rigakafin cutar korona da suka tabbatar da inganci da sahihancin sa.
Wadannan kamfanoni guda tara sun hada da AstraZeneca, BioNTech, GlaxoSmithKline, Johnson & Johnson, Merck, Moderna, Novavax, Pfizer da Sanofi.
Kamfanonin sun ce yanzu da duniya ta matsu a samar da maganin rigakafin cutar korona sun ce za su fitwr da maganin rigakafin ne bayan sun gudanar da gwaje-gwaje bisa ga sharuddan kimiya domin ganin maganin bai cutar da kiwon lafiyar mutane ba.
Discussion about this post