Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 138 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –35, Katsina 44, Kwara 15, Kaduna 13, Plateau 7, Imo 6, Adamawa 5, Rivers 4, Yobe 3, Ogun 2, Oyo 2, Osun 1, FCT 1.
Yanzu mutum 61805 suka kamu da cutar a Naj eriya, mutum 56985 sun warke, 1127 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,693 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 20,768, FCT –5,944, Oyo – 3,423, Edo –2,648, Delta –1,812, Rivers 2,746, Kano –1,741, Ogun – 1,989, Kaduna –2,585, Katsina -948, Ondo –1,659, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 710, Ebonyi –1,049, Filato -3,594, Enugu – 1,314, Abia – 898, Imo – 613, Jigawa – 325, Kwara – 1,050, Bayelsa – 403, Nasarawa – 478, Osun –919, Sokoto – 162, Niger – 274, Akwa Ibom – 295, Benue – 484, Adamawa – 257, Anambra – 277, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 82, Ekiti – 329, Taraba- 122, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Yaran Makaranta 181 da malamansu sun kamu da Korona a wani makaranta a Legas
Akalla dalibai da malaman su 181 ne aka tabbatr sun kamu da Korona da wani makaranta mai zaman kansa a Legas.
Ma’aikatar kiwon Lafiya ta jihar Legas ta sanar cewa yaran makaranta 181 da wasu malaman su sun kamu da Korona a wani makarantar Kwana dake Lekki, Jihar Legas.
Kwamishinan Lafiya na jihar Akin Abayomi, ya shaida cewa bincike da aka gudanar ne ya sa aka gano wadanda suka kamu da cutar.
” Wata daliba ‘yar ajin SSII ce ta fara rashin Lafiya, da aka kaita asibitin makarantar, a nan ne aka gano ta Kamu da Korona. Da aka yi wa daliban makarantar gwaji sai aka gano yara 181 duk sun kamu da wasu daga cikin malaman su.
” Sai dai cutar bata kwantar da su ba dukkan su. Mun shawar ce su da su cigaba da zama a makarantar kada kuma su koma gida su yada cutar, sannan kuma mun tura malaman lafiya su ci gaba da samar da kula a wurin da kewaye.”