Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 118 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum – 41, Rivers-19, Osun-17, Nasarawa-13, Kaduna-5, Anambra-5, Edo-3, Ogun-3, Kwara-3, Ondo-3, Katsina-2, Niger-2, Filato-1 da Akwa Ibom-1.
Yanzu mutum 59,583 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 51,308 sun warke, 1,113 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,162 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 19,692, FCT –5,758, Oyo – 3,273, Edo –2,634, Delta –1,803, Rivers 2,601, Kano –1,738, Ogun – 1,895, Kaduna –2,451, Katsina -894, Ondo –1,638, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 704, Ebonyi –1,042, Filato -3,498, Enugu – 1,289, Abia – 898, Imo – 577 , Jigawa – 325, Kwara – 1,048, Bayelsa – 401, Nasarawa – 468, Osun –864, Sokoto – 162, Niger – 261, Akwa Ibom – 294, Benue – 481, Adamawa – 248, Anambra – 250, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 76, Ekiti – 322, Taraba- 106, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Korona ta kashe mutum miliyan daya a duniya
Sakamakon rahoton ‘Wordometer’ ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar korona ya kashe a duniya ya kai miliyan daya.
A lissafe dai bisa ga rahoton mutum 1,000,502 ne suka mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar.
Mutum 209,000 ne suka mutu a kasar Amurka, kasar Indiya dake bi mata nada mutum 95,000 da suka mutu.
Zuwa yanzu adadin yawan mutanen da Suka kamu da cutar a duniya ya kai mutum miliyan 33.
Duk da haka wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun ce akwai yiwuwar mutanen da suka kamu da cutar da wadanda cutar ta kashe basu a cikin lissafi saboda rashin bincike.
Ranar Asabar kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar cutar za ta kashe mutum miliyan 2 kafin a gano rigakafin ta.
Zuwa yanzu mutum miliyan 24 sun warke daga cutar a duniya.
Nahiyar Afrika
Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC ta bayyana cewa cutar korona ta kashe mutum 35,000 a Afrika.
Zuwa yanzu mutum miliyan 1.4 ne suka kamu da cutar a Afrika.
Kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun ce rashin yin gwajin cutar ne yake sa ba a iya tabbatar da adadin yawan wadanda suka kamu da wadanda suka mutu a Nahiyar ta Afrika.
A Najeriya mutum 58,324 suka kamu da cutar, 49,794 sun warke, 1,108 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,422 ke dauke da cutar.