Idan ba a manta ba a watan da Satumba ma’aikatar ilimi ta sanar cewa gwamnatin tarayyar ta amince wa gwamnonin jihohinnkasar nan su tsaida ranar bude makarantu a kasar nan.
A watan Maris ne gwamnati ta rufe duka makarantun kasar nan a dalilin barkewar annobar Korona a kasa Najeriya da Duniya.
Zuwa yanzu jihohin Legas, Kano, Kaduna Barno, Ogun ,Ekiti da wasu jihohi duk sun sanar da ranakun bude makarantu, wasu ma har sun bude su.
Sai dai kuma dole makarantu su yi taka tsantsan wajen samar wa yara kariya ta hanyar wadata su da abubuwan da ake tsaftace jiki da kuma karantar da su hanyoyin samun kariya a duk lolacin da suka tunkari makaranta.
Ga matakan
1. Makarantu su tabbatar duk wanda zai shiga makaranta sai an yi masa gwajin Korona sannan a duba yanayin zafin jikin sa.
2. A tabbatar duk Wanda zai shiga makaranta ya saka takunkumin fuska.
3. Makaranta ta kebe wasu wurare a makarantar da za a rika wanke hannaye da ruwa da sabulu domin dalibai, malamai da ma’aikatan makaranta.
4. Makarantun kwana su samar da wurin yin gwajin cutar sannan da wurin kebe wadanda tsautsayin kamuwa da cutar ya afka musu.
5. Makarantu zu kebe wuraren da za a kwantar da wani Koda ya kamu da cutar a makarantan.
6. Horas da ma’aikatan lafiya na kowanne makaranta kan yadda za su kula da wadanda suka kamu da cutar tare da Samar wa ma’aikatan kayan kariya.
7. Makaranta za ta nemi izinin iyaye domin kwantar da dalibi koda wani cikin su ya kamu da cutar.
8. Makarantu su tabbata suna kula da tsaftace muhallin su akai akai sannan a watadar da fankoki a ajujuwa domin samun wadatar iska
9. Ajujuwan da ba za a iya saka musu fankoki ba, a tabbata an bude windina domin iska ya riga zagayawa.
10. A rage cinkoson yara a Ajujuwa, sannan a saka su a tsakanin juna da tazara kamar ta mita 1 zuwa 2.
11. Baya ga ruwan wanke hannu, yana da kyau a wadata kowani aji da man tsaftace hannaye. Wanda a duk lokacin da aka dawo daga hutun rabin lokaci, sai dalibi ya goga a hannun sa kafin ya zauna a kujera.
Hukumar Kiyaye Kamuwa da cututtuka ta kasa, NCDC ta sanar da karin mutum 138 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.
Alkaluman da hukumar ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –35, Katsina 44, Kwara 15, Kaduna 13, Plateau 7, Imo 6, Adamawa 5, Rivers 4, Yobe 3, Ogun 2, Oyo 2, Osun 1, FCT 1.
Zuwa yanzu mutum 61805 suka kamu da cutar a Naj eriya, mutum 56985 sun warke, 1127 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,693 ke dauke da cutar a Najeriya.
Discussion about this post