Ministan Abuja, Mohammed Bello ya yi kira ga makarantun gwamnati da masu zaman kansu dake babban Birnin Tarayya, Abuja su koma karatu daga ranar litinin 12 ga Oktoba.
Bello ya ce Tun bayan komawar daliban da ke ajin karshe ba a samu ko da dalibi daya ba da ya kamu da Korona.
Shugaban Kwamitin sake bude makarantu na Abuja, Fatima Abdulrahman ta ce makarantu za su bude duka sannan dalibai duk su koma karatu. Sai dai ta gargadi makarantu da su tabbata sun kiyaye dokokin Korona.
” Duk makarantar da bata bi dokar ba za a hukuntata, sannan kuma ma idan yayi tsanani za a rufe makarantar.
Ta ce dalibai za su rika saka takunkumin fuska, baya ga kiyaye dokiokin korona a makaranta.
Fatima ta kara da cewa a makon farko za a muraji’a ne sannan a mako na biyu kuma dalibai su rubuta jarabawa.
” Daga nan sai a shiga zangon karatu na farko. A wannan shekara babu zangon karatu na karshe. Za a rufe makarantu don hutun Kirismeti ranar 18 ga Disamba.
Jihohin Kano, Edo, Anambra, Oyo duk sun sanar da ranar bude makarantu a jihohin su.
Discussion about this post