Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 179 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –116, Anambra-20, FCT-9, Oyo-9, Rivers-9, Delta-3, Nasarawa-3, Edo-2, Kaduna-2, Ogun-2, Filato-2, Ekiti-1 da Osun-1
Yanzu mutum 60,834 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 52,143 sun warke, 1,116 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,575 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 20,367, FCT –5,858, Oyo – 3,324, Edo –2,639, Delta –1,810, Rivers 2,683, Kano –1,740, Ogun – 1,954, Kaduna –2,522, Katsina -896, Ondo –1,652, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 710, Ebonyi –1,044, Filato -3,547, Enugu – 1,309, Abia – 898, Imo – 585 , Jigawa – 325, Kwara – 1,050, Bayelsa – 403, Nasarawa – 475, Osun –907, Sokoto – 162, Niger – 269, Akwa Ibom – 295, Benue – 483, Adamawa – 254, Anambra – 275, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 325, Taraba- 108, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Korona ta kashe mutum miliyan daya a duniya
Sakamako rahoton ‘Wordometer’ ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar korona ya kashe a duniya ya kai miliyan daya.
A lissafe dai bisa ga rahoton mutum 1,000,502 ne suka mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar.
Mutum 209,000 ne suka mutu a kasar Amurka, kasar Indiya dake bi mata nada mutum 95,000 da suka mutu.
Zuwa yanzu adadin yawan mutanen da Suka kamu da cutar a duniya ya kai mutum miliyan 33.
Duk da haka wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun ce akwai yiwuwar mutanen da suka kamu da cutar da wadanda cutar ta kashe basu a cikin lissafi saboda rashin bincike.
Ranar Asabar kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar cutar za ta kashe mutum miliyan 2 kafin a gano rigakafin ta.
Zuwa yanzu mutum miliyan 24 sun warke daga cutar a duniya.