Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 212 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –85, Oyo-72, FCT-21, Ogun-11, Filato-11, Katsina-6, Kaduna-5, Osun-1
Yanzu mutum 61,194 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 52,304 sun warke, 1,119 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,771 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 20,518, FCT –5,904, Oyo – 3,409, Edo –2,640, Delta –1,810, Rivers 2,689, Kano –1,740, Ogun – 1,969, Kaduna –2,534, Katsina -902, Ondo –1,654, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 710, Ebonyi –1,049, Filato -3,569, Enugu – 1,309, Abia – 898, Imo – 587 , Jigawa – 325, Kwara – 1,050, Bayelsa – 403, Nasarawa – 476, Osun –908, Sokoto – 162, Niger – 269, Akwa Ibom – 295, Benue – 483, Adamawa – 254, Anambra – 275, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 329, Taraba- 109, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Korona ta kashe mutum miliyan daya a duniya
Sakamako rahoton ‘Wordometer’ ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar korona ya kashe a duniya ya kai miliyan daya.
A lissafe dai bisa ga rahoton mutum 1,000,502 ne suka mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar.
Mutum 209,000 ne suka mutu a kasar Amurka, kasar Indiya dake bi mata nada mutum 95,000 da suka mutu.
Zuwa yanzu adadin yawan mutanen da Suka kamu da cutar a duniya ya kai mutum miliyan 33.
Duk da haka wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun ce akwai yiwuwar mutanen da suka kamu da cutar da wadanda cutar ta kashe basu a cikin lissafi saboda rashin bincike.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar cutar za ta kashe mutum miliyan 2 kafin a gano rigakafin ta.
Zuwa yanzu mutum miliyan 24 sun warke daga cutar a duniya.
Discussion about this post