Sakamakon bincike ya nuna cewa yaduwar cutar korona ya ragu zuwa Kashi 50 bisa a kasar nan.
Hakan ya faru ne a dalilin zage damtse da gwamnati ta yi wajen tsananta yin gwajin cutar.
Bisa ga sakamakon gwajin da hukumar NCDC ta fitar ya nuna cewa an samu jimlar mutum 623 da suka kama cutar tsakanin ranar 18 zuwa 24 ga Oktoba.
A wancan makon da ya gabata mutum 1,204 suka kama cutar a kasar nan.
Tun da cutar ta bullo a watan Fabrairu mutum 603,611 be aka Yi wa gwajin cutar a Najeriya.
Hukumar NCDC ta ce Najeriya ta samu ragowa a yawan mutanen dake warkewa daga cutar da yawan dake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar.
Yaduwar cutar Korona a Najeriya
Zuwa yanzu mutum 61,992 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 57,465 sun warke, 1,130 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,397 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 20,789, FCT –5,967, Oyo – 3,421, Edo –2,648, Delta –1,812, Rivers 2,773, Kano –1,742, Ogun – 2,010, Kaduna –2,617, Katsina -952, Ondo –1,666, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 710, Ebonyi –1,049, Filato -3,587, Enugu – 1,314, Abia – 898, Imo – 614, Jigawa – 325, Kwara – 1,067, Bayelsa – 403, Nasarawa – 478, Osun –922, Sokoto – 165, Niger – 274, Akwa Ibom – 295, Benue – 486, Adamawa – 252, Anambra – 277, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 332, Taraba- 122, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Bisa ga yaduwar cutar jihohin Legas, Filato, Oyo, Rivers, Edo da FCT ne suka fi samun yaduwar cutar.
Jihohin Bauchi da Kogi ne jihohin da basu da yawan mutanen da suka kamu da cutar.