KORONA A JIKIN TRUMP: Sakaci da fargabar abin da zai biyo baya

0

Trump ya kamu da cutar Korona ana saura kwanaki 32 a yi zaben shugaban Amurka, a farkon watan Nuwamba. Tuni dai har wasu masu jaben-‘yar-kiri-kiri sun fara jefa ta su kuri’ar.

Trump, dattajo mai shekara 74, shi da matar sa Melania sun shiga sahun Amurkawa sama da milyan 7.3 da suka kamu da cutar Coronavirus, a kasar da cutar ta kashe sama da mutum 200,000.

Kididdigar Alkaluman Bayanan Cutar Korona na Amurka sun tabbatar cewa cikin mutum 100 da cutar ke kashewa a Amurka, to 80 duk dattawa ne ‘yan sama da shekaru 65.

Shekarun Trump 74 a duniya, kuma ya shafe watanni ya na karakainar sa a Amurka ba tare da ya damu ya rika daura takunkumin rufe baki ba.

Abin da ya samu Trump ya girgiza Amurka, ganin hakan ya faru daf da zabe, lokacin da kasar ke fama da mace-mace sanadiyyar barkewar cutar Coronavirus.

Sannan kuma kasar ta kara shiga matsala a daidai lokacin da ake raji da karajin korafin nuna bambanci da wariyar launin bakaken fata. Ga kuma gagarimar annobar gobarar-daji da ke ci gaba da babbake dazukan Yammacin Amurka.

SAKACI, AZAL KO KADDARA?

Yayin da ake fama da cutar Coronavirus a Amurka, fiye da kowace kasa a duniya, kofar shiga Fadar Shugaban Amurka ta bangaren Arewa maso Yamma, ba a daukar mata wasu kwararan matakan hana kamuwa da cutar Coronavirus. Ba a kula da wanda ya daura takunkumi ko wanda bai daura ba.

Ta wannan kofa ce manyan ma’aikatan Fadar White House, Manyan Baki, ‘yan jarida ke shiga farfajiyar fadar mai fadin eka 18.

Kwana biyu kafin a bayyana Trump ya kamu da cutar, Hadimin Yada Labaran sa, Hicks aka fara bayyana cewa ya kamu. Kuma aka killace shi.

Trump ya yi zirga-zirgar yakin neman zabe tare da Hicks a jihohin Pennsylvania, Ohio da Minnesota.

Wadanda ke cikin wannan tawaga su na da yawa. Akwai ma wasu ‘yan jarida da su ka shiga jirgin Trump, Air Force One, aka rankaya da su wannan kamfen. Akwai kuma manyan ‘yan jam’iyya da makusanta da dama.

Manyan likitoci a Amurka sun yi wa jami’an Fadar White House tatas, bisa abin da su ka kira sakacin da aka nuna wajen kare Trump daga kamuwa da cutar Coronavirus.

Likitan Trump da matar sa, Sean Conley ya ce za a ci gaba da killace shugaban da matar sa a Fadar White House. Amma bai ce ko akwai alamun cutar na fitowa a jikin su ba, ko kuma daskararriyar da ba ta nuna alamu ce, sai dai ta rika nukurkusar wanda ta kama.

Tare da ‘yan jarida Trump ya shiga jirgin sa zuwa karon-battar muhawara da Joe Biden a Cleveland. Har yau ba a san yawan mutanen da za a nemi su killace kan su ba, musamman saboda ko a wurin kamfen da filin jirgin sama, ba a cika tsaurara matakan yin nesa-da-juna, gudun kamuwa da cutar Coronavirus ba.

Cutar Korona ta kama Firayi Ministan Birtaniya, Boris Johnson a cikin a
cikin Maris, inda ya shafe kwanaki 20 a killace.

Haka nan kuma ta kama Shugaban Brazil, Jair Bolgonaro mai shekaru 65, shi ma ya shafe kwanaki 20 a killace.

A Brazil Korona ta kama sama da mutum milyan 4.8, ta kashe sama da mutum 145,000.

Abin tambaya ga Trump, shin ko zai bada umarnin a yi masa allurar ruwan sabulun tsaftace hannaye daga kamuwa da cutar Korona, kamar yadda ya rika hakikicewa wai ruwan zai magance Korona a cikin majiyyaci?

Ko kuwa zai kara yi wa Joe Biden gorin cewa shi bagidaje ne, duk inda ya shiga da takunkumi a fuskar sa?

Me zai kasance dangane da tawagar kamfen din Trump?

Share.

game da Author