Ma’aikatar Harkokin Jinai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta bayyana cewa kayan agajin zaman annobar korona da aka gani a wani babban sito a Legas ba nata ba ne.
Minista Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Alhamis.
An rika yada maganganu a soshiyal midiya cewar k kayan agaji mallakar ma’aikatar ne, wai Hajiya Sadiyar ce ta kimshe su ta ki a rabawa ga mabukata.
Amma a martanin da ta yi kan wannan ji-ta-ji-tar, ministar ta ce, “Wannan ba wani abu ba ne illa zuƙi ta malle.
“Hotuna da bidiyoyin da aka dauka daga babban wurin aje kayan sun nuna cewa buhunan shinkafa da sauran an rubuta karara a jikin su cewa ‘Lagos State Government and Ca-Covid’.
“To, ‘Ca-Covid’ a taƙaice na nufin ‘Coalition Against Covid-19’, wanda wata kungiya ce mai zaman kan ta da ta yi hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya, Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Nijeriya, da Cibiyar Lafiya ta Duniya (WHO) da nufin yaki da annobar korona a Nijeriya.”
Ministar ta jaddada cewa ba ma’aikatar ta ba ce ta samo kayan agajin kungiyar ‘Ca-Covid’ tare da rarraba su ko ta taimaka wajen raba su kan wannan tsarin.
Ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da irin wannan labarin, kuma ta ce babu ruwan ma’aikatar da kayan agajin da aka gani a wannan babban sito din na Legas.