Wani bincike ya nuna cewa kashi 1 bisa 3 na ilahirin matan da ke zaman aure a Najeriya, sun taɓa samun sabanin da mazajen su su ka lakada masu dukan tsiya.
Rahoton wanda Dataphye ta fitar, ya nuna yawan matan da mazajen su su ka jijjibga sun kai kashi 36% bisa 100% na yawan matan auren Najeriya.
Rahoton ya kara nuna cewa babu ruwan namiji da cikin da ya dirka wa matar sa, wato ciki komai girman sa bai hana namijin Najeriya suburbuɗar matar sa da dukan tsiya ba.
Akasarin wadanda ake daddalla wa mari ko lakada wa duka ƴan shekaru daga 15 ne zuwa 24.
Haka kuma rahoton ya bada hujjar cewa mazan yankin Arewa maso Gabas sun fi jibgar matan su tamkar jakin falke.
Matan da su ka ci dukan tsiya a cikin yanayin da mazan su sun dirka masu ciki, sun karu sosai daga kashi 4.3% a cikin 2013 zuwa kashi 10.3% a cikin 2018.
Wani babban abin damuwa da rahoton ya bayyana shi ne kusan kashi 1 bisa 3 na matan aure a Najeriya, sai yadda aka yi da su. Ba su da ta-cewa kuma ba su da ra’ayin kan su, sai ra’ayin mazan su.
Kungiyar ‘Dataphye’ da takwarar ta ‘Interactive’, sun yi wannan bibiyar sau da kafar yanayin zamantakewar ma’aurata a Najeriya ne daga kididdigar da Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta fitar a kan jinsin maza da mata a 2013.
Sauran bayanan kuma an hakaito su ne daga rahoton Kididdigar Maza daban da Mata na Najeriya a 2016 zuwa 2017 wanda Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ta fitar.
Rahoton ya ce kusan mata milyan 17 ƴan shekaru daga 15 zuwa 49 sun taɓa tsintar kan su a yanayin da aka yi lalata da su da karfin tsiya.
Har ila yau, rahoton ya ce an fi cin zarafin mata da karfin tsiya a Arewa maso Gabas. Shi ma yankin Kudu maso Yamma, ba a bar shi a baya ba. Shi da yankin Arewa maso Yamma, kusan kankankan su ke. Abin ya yi muni a can.
Kusan kashi 45% na matan jihar Gombe da aka tantance, sun yi korafin an taba cin zarafin su.
Shugaban Dataphye, Joshua Olufemi, ya ce tsawon lokacin da aka shafe ana zaune a gida lokacin korona, ya kara haifar da cin zarafin mata sosai.
Jihar Kebbi ce aka fi samun saukin lakada wa mata duka da kuma cin zarafin su. Inji rahoton.
Discussion about this post