Kasafin Kuɗin 2021: Yadda Muka Aiwatar Da Kasafin 2020 – Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa Sanatoci da Mambobin Majalisar Tarayya cewa Ministar Harkokin Kudade Da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ce za ta yi wa Majalisa bayani dalla-dalla na abin da kowane bangaren kasafin ya kunsa.

Buhari ya fadi haka ne da ya ke gabatar da kasafin kudi na 2021 a zauren majalisar Tarayya ranar Alhamis.

” Mun gabatar da Kasafin 2021 a daidai lokacin da duniya ke fama da gaganiyar annobar cutar korona, wadda sanadiyyar hakan ta haifar da karyewar farashin danyen man fetur, abin da hakan kuma ya kawo cikas ga tattalin arziki.

“Tattalin arzikin Najeriya ya samu tawaya domin karin tattalin arzikin cikin gida (GDP) ya ragu da kashi 6.1 a watanni Afrilu, Mayu, Yuni da Yuli na shekarar 2020. Amma duk da haka, karfin tattalin arzikin Najeriya ya fi na sauran manyan kasashen duniya da kasashe masu tasowa karfin jure dadin kibiyar matsalar da annobar korona ta haifar a duniya.

Daga nan sai ya kara da cewa Gwamnati ta kirkiro aikin-karfi ga matasa 774,000 a fadin kananan hukumomi 774 na kasar nan domin rage kuncin rayuwa.

” Mun kuma kirkiro Shirin Tallafa wa matasa da naira bilyan 75. Tuni ma har an saka naira bilyan 25 daga cikin kudaden Kasafin 2021 domin a fara yin somin-tabi sa su.

” Ku na sane da cewa mun yi wa Kasafin 2020 kwaskwarima sakamakon halin da duniya ta shiga bayan barkewar korona. Hakan ya zama wajibi, kuma mun zabtare kasafin zuwa dala 28 kowace ganga. Mu na hako ganga milyan 1.8 a kullum. Kuma an yi kasafin a kan naira 360 kowace dala daya.

” An yi kiyasin samun naira tiriliyan 5.84 a kudaden shiga a kasafin 2020. Da su aka yi kintacen za a gudanar da ayyukan naira tiriliyan 10.81. Kenan an samu gibi har na naira tiriliyan 4.98, wanda mu ka ce tilas bashi za a rika ciwowa a yi wa jama’a aiki da kudaden.

” Zuwa cikin watan Yuli an tara kudaden shiga naira tiriliyan 2.10.

” Zuwa karshen Yuli kuma an kashe naira tiriliyan 5.37. Kenan an samu gibi na naira tiriliyan 3.27.

” Wannan bai hana mu rika biyan basussukan da hakkin biyan ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya ba. Kuma ana ci gaba da biyan albashi kan kari tare da kashe kudade wajen tafiyar da harkojin gwamnati.

Share.

game da Author