Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba za a biya malaman jami’o’i ko wani ma’aikatacin Gwamnatin Tarayya albashi ba, har sai ya yi rajistar Lambar Tantance Sahihan Ma’aikatan Gwamnati (IPPIS) tukunna.
Buhari ya yi wannan gargadin ne a yayin da ya ke gabatar da kasafin kudin 2021 na naira bilyan 13.08 a gaban daukacin Sanatoci da Mambobin Majalisar Tarayya, ranar Alhamis a Majalisar Tarayya, Abuja.
Ya ce an kirkiro tsarin tantance ma’aikata sahihai ne wato IPPIS domin a hana satar kudi ta hanyar harkalla da zamba, hana biyan ma’aikatan bogi albashi da kuma daukar ma’aikata ana biyan su albashi ba da umarnin gwamnatin tarayya ba.
Wata da watanni kenan malaman jami’a na yajin aiki, saboda rigima da gwamnatin Buhari a kan tsarin IPPIS, wanda su ka ce ba za a yi masu rajistar IPPIS ba.
Yayin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta ce babu ruwan ta da IPPIS, ta ce ta na da na ta tsarin tantance malamai daban.
Shugaban ASSU, Biodun Ogunyemi ya ce ba za su koma makaranta ba, duk kuwa umarnin a koma karatu da gwamnati ta bayar, bayan shafe watanni bakwai dalibai na zaune a gida.
Ogunyemi ya ce ba za su koma ba, domin akwai malaman da ke bin albashin wattanni hudu zuwa shida duk ba a biya su ba.
Ya ce har yanzu gwamnati ba ta kama aniyar magance matsalolin da su ka dabaibaye fannin ilmi a kasar nan ba.
Discussion about this post