KASAFIN 2021: Matsin Korona bai hana Gwamnatin Najeriya ware naira bilyan 2.6 don aikin Hajji da ziyasa Isra’ila ba

0

Duk da kukan rashin kudi da ake yi saboda fantsamar cutar korona da ta haddasa tabarbarewar tattalin arziki, hakan bai hana Gwamnatin Najeriya ware naira bilyan 2 da milyan 600 don aikin Hajji da masu zuwa ziyara Isra’ila ba.

Sai dai kuma kungiyoyin sa-kai sun soki yadda aka ware wadannan makudan kudade, jim kadan bayan buga sanarwar a shafin intanet na Ofishin Tsare-tsaren Kasafin Kudade.

A cikin kasafin, Gwamnatin Buhari ta nemi amincewar Majalisar Tarayya da ta Dattawa ta kashe naira bilyan 2 da milyan 600 wajen gudanar da hidimomin tafiya Hajjin 2021 da kuma dawainiyar Kiristoci matafiya ziyara Isra’ila.

Za a kashe kudaden ne a karkashin Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya da kuma Hukumar Kula da Ziyara Isra’ila ta Kiristoci.

Hukumar Alhazai za ta kashe naira milyan 10 wajen lemun kwalba da kayan zaki da ruwan sanyi da abinci lokacin aikin Hajji.

Sai naira milyan 15 wadda za a kashe wajen raba wa wasu da za a rika gayyatowa jawabai da kuma kudaden alawus din wasu naira milyan 20 don zaman aiki ko taruka, talloli da kuma wayar da kan jama’a.

Bangaren walwala an ware masa naira milyan 70, sai kuma ladar aikin kula da sa-ido kan tafiyar da al’amurra zai lashe naira milyan 30.

A bangaren ziyara Isra’ila kuwa, Hukumar ta ware wasu naira milyan 71.3 domin alawus din tadiye-tafiye tare da sauran abubuwan da su ka jibinci tafiye-tafiyen da za su lashe naira milyan 586.5

Za a kashe naira milyan 42.3 wajen sayen kujeru da tebura da aikin kula da gidajen kwana.

Akwai wasu naira milyan 181.6 da aka ce za a kashe domin ayyukan da ka iya tasowa.

Sai dai kuma kungiyoyi sun ki yin na’am da kasafin, musamman su ka yi rika yin sharhi kan kasafin.

Da yawa na ganin cewa wadanan kudade naira bilyan 2.6, za a iya gina ajujuwan sakandare tare da sa musu kujeru da tebura, har aji 260. Sannan kuma a bi makarantun a damka musu naira milyan 10 kowace.

Share.

game da Author