A kasafin kudin da shugaba Buhari ya gabatar a majalisa ranar Alhamis, ya karawa majalisar kasa kudi fiye da na ma’aikatar tsaro akan kasafin bara.
Shugaba Buhari ya ware wa majalisar kasa naira biliyan 128 wanda a shekarun baya naira biliyan 125 ne aka ware musu.
Sun samu karin naira biliyan 3 a kasafin 2021.
A shekarar 2020, an ware wa ma’aikatar tsaro naira biliyan N878.4 amma a kasafin 2021 an ware mata naira biliyan 840.56 ne kacal.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa Sanatoci da Mambobin Majalisar Tarayya cewa Ministar Harkokin Kudade Da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ce za ta yi wa Majalisa bayani dalla-dalla na abin da kowane bangaren kasafin ya kunsa.
Buhari ya fadi haka ne da ya ke gabatar da kasafin kudi na 2021 a zauren majalisar Tarayya ranar Alhamis.
” Mun gabatar da Kasafin 2021 a daidai lokacin da duniya ke fama da gaganiyar annobar cutar korona, wadda sanadiyyar hakan ta haifar da karyewar farashin danyen man fetur, abin da hakan kuma ya kawo cikas ga tattalin arziki.
“ Tattalin arzikin Najeriya ya samu tawaya domin karin tattalin arzikin cikin gida (GDP) ya ragu da kashi 6.1 a watanni Afrilu, Mayu, Yuni da Yuli na shekarar 2020. Amma duk da haka, karfin tattalin arzikin Najeriya ya fi na sauran manyan kasashen duniya da kasashe masu tasowa karfin jure dadin kibiyar matsalar da annobar korona ta haifar a duniya.
Daga nan sai ya kara da cewa Gwamnati ta kirkiro aikin-karfi ga matasa 774,000 a fadin kananan hukumomi 774 na kasar nan domin rage kuncin rayuwa.
” Mun kuma kirkiro Shirin Tallafa wa matasa da naira bilyan 75. Tuni ma har an saka naira bilyan 25 daga cikin kudaden Kasafin 2021 domin a fara yin somin-tabi sa su.
Discussion about this post