KASAFIN 2020: Yadda za a cike gibin naira 5.2 – Ministar Kudi

0

Gwamnatin Najeriya za ta ciwo basussuka daga wajen Najeriya da kuma cikin kasa domin cike gibin naira tiriliyan 5.2 da za a samu a kasafin 2021.

Ministar Harkokon Kudade Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, ta kara da cewa a waje za a ramto kudade daga kungiyoyin kasashe masu hada-hadar kudade da cibiyoyi da bankuna.

Haka Ministar Harkokin Kudade da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta bayyana a ranar Talata, lokacin da ta ke gabatar wa Majalisa dalla-dallar abin da kasafin na 2021 ya kun sa.

Ta ce yayin da za a ciwo bashin naira tiriliyan 2.14 a nan gida da kuma wata naira tiriliyan 2.14 daga waje, haka nan kuma za a kara ciwo bashin naira bilyan 707.69 daga kungiyoyin kasa da kasa.

Sai kuma naira bilyan 206.16 da ake sa ran samu daga cefanar da wasu kadarorin gwamnatin tarayya da za a yi.

Sauran hanyoyin samun kudaden da za a cike gibin kasafin kuma ya hada sayar da wasu masana’antu na gwamnati.

A ranar da ya gabatar da Kasafin 2021, Buhari ya ce gwamnatin sa za ta ciwo wa Kasafin 2021 bashin naira tiriliyan 4.28.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a samu gibin naira tiriliyan 4.28 a Kasafin 2021.

Da ya ke bayanin yadda za a cike gibin, Buhari ya shaida wa gamayyar majalisin Dattawa da Mambobin Tarayya cewa bashi za a ciwo domin a yi wa al’umma ayyukan raya kasa, saboda kudaden shigar da Najeriya ta yi hasashen tarawa, ko kadan ba za su isa a yi manyan ayyukan da su ka kamata a yi da su ba.

Buhari ya ce cikin 2021 za a kashe naira bilyan 501.19 wajen biyan kudaden fanshon tsoffin ma’aikata.

Ya ce za a kashe naira tiriliyan 3.124 wajen biyan basussukan da su ka yi wa Najeriya katutu.

Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta (NDDC) za ta samu naira bilyan 63.51. Hukumar Farfado da Yankin Arewa maso Gabas za ta samu naira bilyan 29.70, sai Hukumar Bunkasa Ilmi a Matakin Farko (UBE) ta za samu naira bilyan 70.

Za a bai wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) naira bilyan 40, sai Majalisun Dattawa da ta Tarayya naira bilyan 120.

Share.

game da Author