Gwamnan jihar Ribas ya yi kira ga Iyaye da kakkausar murya ce wa su ja wa ƴaƴan su kunne tunda wuri kada wani ya sake fitowa titunan jihar da sunan yin zanga-zanga abin da aka rusa.
Wike ya ce duk wanda ya saba wannan doka toh, ya kuka da kansa.
” Wani zanga-zanga kuma za a fito yi bayan gwamnati ta rusa rundunar SARS din. Za a yi zanga-zanga akan abinda babu ne? Kowa ya shiga taitayin sa domin duk wanda ya karya doka zai dandana kuɗar sa.
Idan ba a manta ba har yanzu wasu a jihohin kasar nan musamman yankin kudu maso yamma na cigaba da zanga-zanga duk da gwamnati ta bi yadda suke so ta rusa rundunar SARS din.
A jihar Legas har fito na fito aka yi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga.
Rundunar Ƴan sandan jihar ta zargi wasu daga cikin masu zanga-zangar da yin amfani da bindigogi.
A jihar Oyo ma matasa sun ci gaba da yin zanga-zanga da yin arangama da jami’an ƴan sanda.
Jihar Anambra da Abia suma sun cigaba da gudanar da zanga-zangar duk da rusa SARS da gwamnati ta yi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce baya ga rusa wannan runduna, za a yi wa jami’an tsaro na ƴan sanda garambawul domin kauce sake faruwan irin haka.