Jihar Gombe za ta yi wa mutum 500,000 gwajin Ƙanjamau

0

Gwamnatin jihar Gombe ta gudanar da taro domin yi wa mutum 500,000 gwajin cutar ƙanjamau a jihar.

Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Ahmed Gana ya Sanar da haka a wajen taron.

Gana ya ce idan aka yi haka za a samu raguwar yaduwar cutar a jihar.

Idan ba a manta ba a watan Satumba hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau ta kasa NACA ta kaddamar da sabbin na’urorin gwajin cutar masu suna ‘WONDFO HIV 1 and 2 Rapid Test Kit’.

Shugaban hukumar Gambo Aliyu, yace na’urorin yin gwajin zasu taimaka wajen ganin burin gwamnati ya a cika na yi wa mutane da yawa gwajin cutar a kasar nan.

Akwai rahohon da aka bayyana a wannan shekara da ke bayanin yadda mutane da dama ke dauke da cutar a kasarnan kuma ba su cikin wadanda ake da su cikin jadawalin masu fama da cutar a kasar.

Share.

game da Author