Gwamnati jihar Barno ta sanar da sanara da buɗe duka makarantun jihar daga ranar 26 ga Oktoba.
Kwamishinan ilimin jihar Bello Ayuba, ya sanar da haka ranar Litinin.
Ayuba ya ce makarantu za su ci gaba da zama a rufe har sai ranar 26 ga Oktoba.
Ya ce gwamnati za ta tabbatar cewa masu makarantu sun saka matakan guje wa kamuwa da cutar Korona makonni biyu kafin dalibai su fara zuwa makaranta.
“Gwamnati ta yi wa makarantun sakandare 84 dake jihar feshi sannan za ta tanadi kayan guje wa kamuwa da cutar Korona domin rabawa wa makarantu.
“Gwamnati za ta tabbatar duk makarantu sun samar da wurin yin gwajin cutar sannan ta samar da takunkumin fuska, man tsaftace hannaye da sauran su.
“Gwamnan jihar Babangana Zulum ya yi kira ga makarantu da su kiyaye dokokin guje wa kamuwa da cutar domin kare kiwon lafiyar dalibai da malamai.
Bayan haka Ayuba ya ce kiyaye dokar bada tazara tsakanin mutum da mutum ba zai yi wahala ba saboda daliban dake ajin karshe sun kammala rubuta jarabawa kuma sun koma gida.
Idan ba a manta ba gwamnati ta rufe duk makarantu a kasar nan domin hana yaduwar cutar Korona.
Bayan haka gwamnati ta bada umurnin a bude makarantu domin daliban dake ajin karshe su rubuta jarabawar su ta karshe.
Daga nan kuma gwamnatin tarayya ta bai wa jihohi damar tsayar da ranar bude makarantu a jihohin su ganin yadda yaduwar cutar korona ya ragu a kasan.
Zuwa yanzu jihohin Kano, Legas sun tsayar da ranar bude makarantu a jihohinsu.
Zuwa yanzu mutum 745 suka kamu da cutar Korona a jihar Barno.
Mutum hudu na kwance a asibiti, 705 sun warke sannan 36 sun mutu.
Discussion about this post