Iyan Zazzau Bashar Aminu ya maka gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu mutum Tara a kotu yana kalubalantar nadin Ahmed Bamalli sabon Sarkin Zazzau.
Idan ba a manta ba, a makon jiya ne gwamnan jihar Kaduna ya nada Ahmed Bamalli sarkin Zazzau, bayan shafe kwanaki 17 ana sauraren sabon sarki.
Iya Bashar ya roki kotu ta soke nadin Bamalli da gwamna El-Rufai yayi cewa hakan ya saba wa yadda aka saba nadin sabon sarki idan sarki ya rasu. kuma shine ya cancanta zama sabon Sarki ba Bamalli ba.
Bayan haka ya roki kotu ta tabbatar da zabin masu zaben sarki na masarautar Zazzau wanda ya sa shi kan gaba cikin wadanda suka nemi sarautar.
Sannan ya ce kotu ta tabbatar masa da sarautar Zazzau tunda shine masu zaben sarki suka zaba.