IPPS: Duk malamin jami’ar da ba ya cikin rajista nan da Nuwamba, zai yi asarar albashin sa – Gwamnatin Tarayya

0

Gwamnatin Tarayya ta sake yi wa malaman Jami’o’in Gwamnatin Tarayya gargaɗin cewa ta ba su wa’adin nan da watan Nuwamba kowa ya yi rajista da tsarin tantance karɓar albashi na IPPIS ko kuma su yi asarar albashin su.

Wata sanarwar wasika da aka aika wa dukkan Shugabannin Jami’o’in Gwamnatin Tarayya (VC), an umarce su da su kara sanar da malaman cewa za a cire sunan duk wanda bai yi rajista da IPPIS ba daga tsarin biyan albashi.

Takardar wacce Daraktan Tsarin IPPIS na Ofishin Akanta Janar na Najeriya, Nsikak Ben ya sa wa hannu, ta ce duk malamin jami’ar da “bai samu yin rajista ta IPPIS ba, saboda dalilin ya tafi hutu, ko zaman jiyya asibiti ko haihuwa kuma bai samu damar yin rajistar IPPIS to ya gaggauta yi zuwa Nuwamba.

“Idan Nuwamba ta yi bai yi rajista ta, zai rasa albashin sa, har sai ya je Ofishin IPPIS a Ofishin Akanta Janar, tare da fam mai ɗauke da shaidar Shugaban Makaranta sannan a amince da shi.

“Sannan kuma sai ya hada da kwafen takardar shaidar ƙarbar albashi na akalla watanni shida baya.” Inji sanarwar.

Ko a jawabin sa na gabatar da Kasafin Kudaden 2021, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargaɗin lallai sai malamin jami’a ya ‘rataya layar IPPIS’ sannan za a biya shi albashi -Buhari.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba za a biya malaman jami’o’i ko wani ma’aikatacin Gwamnatin Tarayya albashi ba, har sai ya yi rajistar Lambar Tantance Sahihan Ma’aikatan Gwamnati (IPPIS) tukunna.

Buhari ya yi wannan gargaɗin ne a yayin da ya ke gabatar da kasafin kuɗin 2021 na naira bilyan 13.08 a gaban ɗaukacin Sanatoci da Mambobin Majalisar Tarayya, ranar Alhamis a Majalisar Tarayya, Abuja.

Ya ce an ƙirkiro tsarin tantance ma’aikata sahihai ne wato IPPIS domin a hana satar kudi ta hanyar harkalla da zamba, hana biyan ma’aikatan bogi albashi da kuma daukar ma’aikata ana biyan su albashi ba da umarnin gwamnatin tarayya ba.

Wata da watanni kenan malaman jami’a na yajin aiki, saboda rigima da gwamnatin Buhari a kan tsarin IPPIS, wanda su ka ce ba za a yi masu rajistar IPPIS ba.

Yayin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta ce babu ruwan ta da IPPIS, ta ce ta na da na ta tsarin tantance malamai daban.

Shugaban ASSU, Biodun Ogunyemi ya ce ba za su koma makaranta ba, duk kuwa umarnin a koma karatu da gwamnati ta bayar, bayan shafe watanni bakwai dalibai na zaune a gida.

Ogunyemi ya ce ba za su koma ba, domin akwai malaman da ke bin albashin wattanni hudu zuwa shida duk ba a biya su ba.

Ya ce har yanzu gwamnati ba ta kama aniyar magance matsalolin da su ka dabaibaye fannin ilmi a kasar nan ba.

Share.

game da Author