INEC ta shirya wa zaben gwamnan Ondo, duk da gobarar wasu kayan aiki a jihar – Farfesa Yakubu

0

Shugaban Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ta gama duk wani shiri don gudanar da zaben gwamna da za a yi a Jihar Ondo a ranar Asabar mai zuwa, 10 ga Oktoba, 2020.

Farfesa Yakubu ya ce, “Hukumar ta shirya wa zaɓen. Yau kwana na biyu a nan Jihar Ondo ina duba shirye-shiryen da mu ka yi kuma na gamsu da abin da na gani.”

Shugaban ya bada wannan tabbacin ne a wajen wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki a wani babban zauren taro da ake kira Dome International Culture and Event Centre a birnin Akure a ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2020.

Ya yi wannan bugun ƙirjin ne duk da yake an yi wata gobara wadda ta lakume injinan karanta katin zabe kamar yadda aka fada a labarai kwanan nan.

Farfesa Yakubu ya kara da cewa,  “Game da gobarar nan abin bakin ciki da ta faru wadda a watan jiya ta cinye dukkan injinan mu na karanta katin zabe a Jihar Ondo, mun kawo isassun madadin su daga Jihar Oyo kuma mun sake saita su don zaben da za a yi ran Asabar. Mun yi isasshen shiri tare da Hukumar ‘Yan Kwana-kwana ta Kasa don tabbatar da cewa irin wannan abu bai ƙara faruwa ba.”

Yayin da ya ke lissafa irin matakan da aka dauka don samun gudanar da zaben ranar Asabar cikin nasara, Farfesa Yakubu ya ce, “Mun dauki dukkan ire-iren ma’aikatan wucin gadi da mu ke bukata, mun horas da su, mun tantance su, saboda zaben. Mun kai kayan aiki marasa hatsari zuwa dukkan Kananan Hukumomi guda 18 na Jihar Ondo. Mun gargadi ma’aikatan mu (na wucin gadi da na dindindin) da su yi aiki bisa kwarewa kuma ba tare da wariya ba wajen gudanar da ayyukan da aka dora masu. Ana ci gaba da aikin wayar da kai da fadakar da masu zabe.

“Mun gama shirin kwasar ma’aikata da kayan aiki zuwa wuraren zabe a dukkan rumfuna 3,009 da mazabu 203 da ke faɗin jihar.

“Yau da yamma, Babban Bankin Nijeriya zai kai dukkan kayan aiki masu hatsari zuwa reshen sa na Akure.”

Ya ce: “Mu na ci gaba da aiki kafada da kafada tare da hukumomin tsaro a karkashin Kwamitin Tuntubar Hukumomi kan Tsaro a Zaben (Inter-Agency Consultative Committee on Election Security, ICCES) don tabbatar da yin zaben cikin kwanciyar hankali da tsaro a ranar 10 ga Oktoba.”

Ya mika godiya ta musamnan ga dukkan hukumomin da ke cikin ICCES, musamman jagorar hukumomin, wato rundunar ‘Yansandan Najeriya, saboda yadda su ke ci gaba da bada goyon baya da aiki cikin kwarewa a lokacin da ake shirin zaben.

Shugaban na INEC ya kuma fadi cewa: “Tun daga lokacin da Hukumar ta fitar da jadawalin ranaku da ayyukan zaben gwamna na Jihar Ondo watanni takwas da su ka gabata a ranar 6 ga Fabrairu, 2020, mun yi ta aiki tare da jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su a wajen tarurruka daban-daban. Kuma mun yi ta musayar ra’ayoyi da hukumomin tsaro a matakin kasa da na jiha.

“Mun yi tuntuɓa tare da neman goyon baya da addu’ar Majalisar Sarakuna ta Jihar Ondo. Mun zauna da shugabannin addini, kungiyoyi masu zaman kan su da kuma kafofin yada labarai.

“Mun tattauna da Kwamitin Wanzar da Lumana na Kasa (National Peace Committee) da ke ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Kasa Abdulsalami A. Abubakar,, wanda ya gayyato jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar don su zauna su rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya a nan Akure gobe.”

Farfesa Yakubu ya ce, “Babban burin mu shi ne mu tabbatar da cewa zaɓmbar wanda zai zama Gwamnan Jihar Ondo gaba daya ya na hannun masu zabe.

“Ina so in tabbatar wa da dukkan masu zaɓe cewa kowace kuri’a da za a kada za ta yi tasiri kuma wanda jama’ar Jihar Ondo su ka zaɓa kadai ne zai kasance sakamakon zaben.

“Ina so in tabbatar wa da jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su cewa za mu ci gaba da kasancewa masu bin dokoki da ka’idojin aikin mu.

“Bari in kara tabbatar wa da dukkan masu ruwa da tsaki cewa Hukumar Zaɓe ba za ta dauki kowane irin mataki don ta dadada ko bakanta wa wata jam’iyyar zaɓe ko dan takara ba.

“Hukumar ta yi nazarin yadda ta gudanar da zaben gwamna kwanan nan a Jihar Edo. A shirya mu ke mu ci gaba da inganta aikin mu. Saboda wannan dalilin, mun gano wurare 16 da ke buƙatar inganta aiki, wadanda su ka haɗa da kayan aiki, daukar mataki kan injin zaben da ya samu matsala cikin gaggawa a Ranar Zabe, matsalar sayen ƙuri’a a lokacin zabe, da kuma bin dokokin kare kai daga cutar korona.

“Don haka, mun dauki hayar motoci da jiragen ruwa na sufuri don kai da kawon kayan aiki a wurare masu tsandauri da kuma wadanda ke yankunan da ruwa ya ke.

“Mun kara daukar ma’aikatan wucin gadi guda 104 don bada tallafi a yankunan da masu zabe su ka yi rajista don su yi aikin gaggawa kan injinan karanta kati a Ranar Zabe.”

Share.

game da Author