Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta ɗage dukkan zabubbukan cike gurbi da ta shirya yi a jihohi 11 na kasar nan.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, kakakin hukumar, Festus Okoye, ya ce an dakatar da gudanar da zabubbukan cike gurabe 15 saboda halin rashin tsaro da ake ciki yanzu.
A da an shirya yin zabubbuuka shida na sanatoci da kuma tara na majalisun jihohi a ranar 31 ga Oktoba.
Zanga-zangar Allah-wadai da ta’asar ‘yansandan SARS karkashin yekuwar #EndSARS dai ta rikide ta zama tarzoma wadda har da kashe rayuka a sassan kasar nan.
“INEC ta yi taro a ranar 22 Ga Oktober, 2020 tare da dukkan Kwamishinonin Tarayya 37 domin nazarin zabikan cike gurabu 15 da za a yi a jihohi 11 na kasar nan, a ranar 31 Ga Oktoba, 2020.
“A kan haka ne aka zartas da dage zabubbuka a Shiyyar Sanata 6 da kuma Mazabun Jihohi 9, bisa yadda Sashe na 26 (2) na Dokar Zabe ta 2010 (mai kwaskwarima) ta gindaya, kuma ta bai wa INEC karfin ikon aiwatarwa.
“INEC za ta ci gaba da sa-ido da duban yadda lamarin ke gudana, inda nan da makonni biyu za ta sake taro domin sa ranar da za a yi zabubbukan.” Inji Okoye.