Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya yi kira da a sauya tsarin yadda ake yin zabe yanzu daga na hannu zuwa na komfuta, wato ‘electronic system’.
Ya yi wannan kiran ne a wajen taron kaddamar da Kwamitin Musamman Na Yi Wa Tsarin Mulkin 1999 Garambawul wanda Majalisar Wakilai ta kafa, a Abuja ran Alhamis.
Farfesa Yakubu ya ce tsarin yadda ake zaɓe a Najeriya a yau ya zama tsohon yayi matuka, wanda saka hannu ya yi yawa cikin sa.
Ya kara da cewa lallai ne a yi gyaran da zai bada damar shigo da tsarin yin zabe ta hanyar komfuta a cikin tsarin gudanar da zane a lasar nan.
Ya ce, “Kun dai Ga nasarar da mu ka samu a Edo inda mu ka samu damar tura sakamakon zabe ta hanyar komfuta; saboda haka tilas ne a cire wannan waigin.”
Haka kuma ya yi kira da a kafa hukumar hukunta masu aikata laifuffukan zane, ya na mai karawa da cewa yi wa tsarin mulki kwaskwarima zai bada hanyar da za a rika bi ana hukunta masu aikata laifuffuka a lokacin zabe a kasar nan.
Ya ce akwai kwamitoci da dama a baya wadanda su ka yi ƙoƙarin ganin an kafa hukumar hukunta masu aikata laifuffukan zaɓe, amma hakar su ba ta cimma ruwa ba.
Yakubu ya ce kafin a yi babban zaɓen shekarar 2015, INEC ta fito da wani tsari na musamman wanda ya shardanta cewa za a riba gudanar da zane ne a ranar Asabar ta biyu ta watan Fabrairu.
A cewar sa, haka ake yi a Amurka da Ghana inda su ke da rana ta musamman da su ka kebe don gudanar da zane.
Ya ce, “Idan aka dauki wannan matakin, daga yau zai kasance sauran kwana 855 kafin babban zabe kenan; saboda haka ba mu da isasshen lokacin da za a yi wa tsarin mulkin garambawul.”
Babban bako mai jawabi a taron, Farfesa Dakas Dakas, ya yi ga kwamitin da ya dubi al’amurran bai wa jama’ar kasa damar tofa albarkacin bakin su, da batun sake fasalin zamantakewar siyasar kasar, da kuma batun karka-karbar mulki, da sauran su.
Ya yi kira ga kwamitin da ya tabbatar a aikin garambawul ɗin sun samar da tsarin mulkin da zai kasance da gaske na ‘yan Nijeriya ne.
Ya kara da cewa muhimmancin samar da tsarin mulki wanda kowa zai yi na’am da shi babban lamari ne wajen dorewar Nijeriya.
Dakas, wanda farfesan ilimin shari’a ne, ya yi kira ga ‘yan majalisar da su guji fadawa cikin matsaloli a kokarin su na yi wa tsarin mulkin 1999 kwaskwarima, ya na mai nanata cewa su fi maida hankali wajen ganin sun samar da tsarin mulki na dukkan jama’a.
Ya jaddada cewa bukatar da ke akwai ta tabbatar da cewa akwai sa hannun kowa tare da saka wa kowa shaukin amincewa da aikin da za a yi shi zai samar da nasara.
Ya kara da cewa tilas ne a kauce wa kurakuran da aka yi a baya.
Ya ce, “Ganin cewa a baya wajen aikin yi wa tsarin mulki garambawul mun ci karo da yunkurin cusa ajandar tazarce karo na uku, wanda a karshe ya rusa dukkan aikin, yanzu akwai ‘yan Nijeriya da dama da su ke tunanin ko akwai bukatar yin shi wannan aikin.
“Saboda haka, akwai bukatar a sa ‘yan Nijeriya su aminta da aikin kuma a nuna masu cewa za a yi aiki ne mai aminci kuma wanda ya yi daidai da bukatun su.”
Ya ce akwai bukatar a samu goyon bayan kafafen yada labarai, na gargajiya da kuma soshiyal midiya, ya kara da cewa ya dace kwamitin ya sadu da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da kungiyoyi masu zaman kan su (CSOs).
Haka kuma Dakas ya ce kwamitin ya hadu da kungiyoyin addini, da Majalisun Dokoki na jihohi da sauran manyan masu ruwa da tsaki domin samun ra’ayoyin su kan aikin garambawul din.
Ya ce tilas ne a yi watsi da ra’ayoyi marasa kangado da na son rai, ya ƙara da cewa kada a bari batun addini da na kabilanci su shigo cikin aikin.
A cewar sa, “Kada ku wuce gona da iri a fasalin tsarin mulki, sannan ku guji girman kai na giyar mulki ta hanyar kafa misali da karfin misalin ku, ba kafa misali da karfin mulkin ku ba.”