Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya sha alwashi da tabbatar wa mutanen jihar Katsina cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gama da Ƴan ta’adda a Katsina da kasa baki ɗaya.
Aregbesola ya kara da cewa shugaba Buhari ya maida hankali matuka wajen ganin an kawo karshen hare-haren miyagun mutane da duka addabi kasar nan.
Ministan ya cigaba da fadi wa wadanda suka halarci taron da ka yi a Katsina cewa gwamnaticin baya sun yi nasara akan mahara kuma shima Buhari zai yi wannan nasara.
A karshe yayi kira ba mutane da su ba jami’an tsaro hadin kai da karfin guiwa domin samun nasara.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arrwa Maso Yammacin kasar nan dake fama da hare-haren ƴan ta’adda.
Baya ga jihar Kaduna da Zamfara da abin yayi kamari, jihar Katsina ma na ciki ki tsundum.
A kwanakin baya har garin Daura mahara suka dira, suka arce da magajin garin Daura.
Jami’an tsaro sun ceto bayan shafe watanni kusan uku tsare a hannun maharan.