Babban Faston Cocin Living Faith, David Oyedepo ya bayyana goyon bayan sa ga Zanga-zangar #EndSARS da ke gudana a fadin kasar nan a yanzu.
Dubban matasa a fadin kasar nan na yin zanga-zangar #EndSARS a musamman jihohin yankin kudancin Najeriya da Abuja.
A kullum sai sun datse manyan tituna da kasuwannin a jihohin da zanga-zangar ta yi tsanani.
Sai dai kuma gwamnati ta saurari korafin matasan, ta rushe rundunar SARS din amma bai hana su cigaba da zanga-zangar ba.
Oyedepo ya ce dama can ya taba yi wa gwamnati gargaɗin haka tun a 2015.
” Na ja wa gwamnati kunne tun a 2015, cewa na hango bala’i da kata’i da zai kunno kai a kasar nan, kuma na yi ta yi mata gargaɗi amma an yi min kunnen-uwar-shegu. Najeriya bata taba fadawa yanayi irin haka ba da ake kashe-kashen rayuka babu kakkautawa irin shekaru biyar da suka wuce.
” Duk wata tsari na gwamnati da bata damu da yadda ake kashe-kashen rayukan mutanen ta ba, bata da amfani kwata-kwata. A dalilin haka matasa suka fusata yanzu.
Sai dai kuma abinda ya bambamta shine a yankin Arewacin Najeriya kaf, babu jiha daya da ta ke goyon bayan wannan zanga-zanga.
A jihar Barno ma kira suka yi da gaba daya kaf an turo musu ƴan SARS dinne jihar.
Har a kasashen waje ana yin wannan zanga-zanga na #EndSARS.