Ɗaya daga cikin lauyoyin da ke kare dakataccen Shugaban Riko na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, mai suna Zainab Abiola, ta garzaya Babbar Kotun Abuja, inda ta yi rantsuwar ikirarin cewa Shugaban Kwamitin Binciken Magu, Ayo Salami ya shaida musu cewa ya na da-na-sanin karbar shugabancin kwamitin binciken Magu.
PREMIUM TIMES ta samu kwafen rantsuwar-kaffarar-kwansitushin da Zainab ta yi, inda ta rantse a kotu cewa tabbas Tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara na Najeriya, Ayo Salami ya yi ikirarin.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga cewa Lauyoyin Magu sun ce tabbas Salami ya ce ya yi da-na-sanin shugabancin Kwamitin Binciken Magu.
Ɗaya daga cikin lauyoyin dakataccen Shugaban Riko na Hukumar EFCC Ibrahim Magu, ya jajirce cewa tabbas Mai Shari’a Ayo Salami ya furta a gaban su cewa ya na da-na-sanin shugabancin kwamitin binciken Magu da aka dora masa nauyi.
PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa lauyoyin Magu biyu, Zainab Abiola da Tosin Ojaoma, sun yi ikirarin cewa Salami ya yi wannan furucin a ranar da su ke kammala gabatar da kare Magu a gaban kwamitin.
Kwamitin dai ana daukar duk bayanan komai a kyamara, a dukkan zaman da ya ke yi a Fadar Shugaban Kasa.
Bayan buga labarin cewa Salami ya yi da-na-sani, tsohon Cif Jojin Najeriya din ya fitar da takardar karyata lauyoyin, inda ya ce shi bai taba cewa ya yi da-na-sanin shugabancin kwamitin binciken Magu ba.
Ya ce lauyoyin karya su ka kantara masa. Amma dai har yanzu bai yi wata barazanar maka su kotu ba, tin bayan karyatawa da ya yi, makonni biyu da su ka gabata.
“Ba ni da wani dalilin da zai sa a ce wai ina da-na-sanin karbar shugabancin kwamitin binciken Magu da na yi.”
Haka ya bayyana cikin wata takardar da ya fitar ga manema labarai, kuma ya sa mata hannu da kan sa.
“Ban taba lauyoyin biyu ko wani ko wasu su fita kafafen yada labarai su yi magana a madadi na ba. Saboda na san a matsayi na na tsohon Cif Jojin Kotun Daukaka Kara ta Kasa, to zan iya bayyana abin da ke raina a ko’ina. Ba sai na tsaya wakilta wani ya yi magana a madadi na ba.
“Na sha warware kulli ko shari’ar da ta fi wannan tsauri. Saboda haka wannan kage ne da sharri kawai aka yi min domin a bata min suna.”
Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tuntubi Ojaoma dangane da karyata su da Salami ya yi, sai ya ce tabbas Salami ya yi furucin, domin ya wuce ya kantara wa Salami karya.
“Kai ni fa a shirye na ke na yi rantsuwar kaffarar kwansitushin a kotu (wato affidavit).”
An tambaye shi su wa da su wa ke wurin, yayin da Salami ya yi furucin, sai ya ce akwai su lauyoyin Magu da kuma dukkan mambobin kwamitin binciken Magu, wadanda Salami ne shugaban su.
Ya kara da cewa babban lauyan Magu Wahab Shittu ma ya na wurin a lokacin.
PREMIUM TIMES ta kasa samun Shittu kafin buga wannan labari.
‘RANTSUWAR-KAFFARA’: Kwafen rantsuwar da Zainab ta yi a ranar Juma’a, 2 Ga Oktoba, ya na kuntse da rubutacciyar rantsuwa cewa:
“Na rantse Shugaban Kwamiti Ayo Salami ya furta cewa, “Ina da-na-sanin shugabancin wannan kwamiti. Na yi ritaya tun cikin 2013, na koma gida ina zama na. Wai duk me ya kawo wannan ne? Abin nan abin kunya ne. Abin kunya ne kam.
“Lauya Tosin Ojaoma ta tashi ta je wurin sa ta ce masa, kada ya damu. Ai aikin kasa da aikin jama’a ne zai yi. Don haka ba abin da-na-sani ba ne.”
Zainab bayan ta rantse, ta kuma yin bayanin cewa idan ana tababa, a binciki kyamarar CCTV da aka kak-kafa a Fadar Shugaban Kasa, za su bayyana komai.
Ranar Litinin Lauya Tosin Ojaoma za ta je Babbar Kotun Abuja ita ma ta rantse.
Abin Da Ke Tattare Da Rantsuwa:
1. Idan har aka tabbatar cewa Ayo Salami ya ce ya na da-na-sani, to dayan biyu – ko dai ayyukan binciken da ya yi za su shiga zargin cewa an nada shi ya biya wata bukata ce, ko kuma ya karba ba da son ran sa ba.
2. Idan kuma aka tabbatar bai fada ba, to lauyoyin Magu sun yi kazafi days to sharri a kan sa, domin su zubar da martaba da kimar sakamakon binciken kwamitin.
Wasu lauyoyin da PREMIUM TIMES ta zanta da su, sun hakkake cewa tun farko bai ma kamata a yi binciken a asirce ba.