Hukumar NNPC ta yi asarar naira bilyan 20 cikin 2019 -Rahoto

0

Kamfanin NNPC na Najeriya ya sibga asarar naira bilyan 20.2, cikin 2019, kamar yadda rahoton da masu binciken kudade su ka fitar.

Cikakken bayanin karshen shekara a ranar 31 Ga Disamba, 2019 NNPC ya yi asarar naira bilyan 16.3, yayin da gaba dayan jimillar rukunin hukumomin da ke karkashin sa sun yi asarar naira bilyan 20.2.

Idan ba a manta ba, ko cikin 2018 sai da NNPC ya dibga asarar naira bilyan 203.2.

Amma rahoton ya ce wannan yawan asara da NNPC ke yi cikin shekarun nan, sun kai naira tiriliyan 1.55 da kuma wasu naira bilyan 474.

Kenan asarar ta kai naira tiriliyan 1.6 ya zuwa 2018.

Rahoton ya nuna cewa kamfanin NNPC zai iya durkushewa ganin yadda yadda ya ke yawan narka asarar makudan kudade.

A kamfen din zaben 2019, Atiku Abubakar ya sha alwashin saida NNPC ga masu hannun jari idan ya ci zabe.

An rika yi masa yarfe a kan ikirarin sa na zai sayar da NNPC.

Sai kuma ga shi a farkon Satumba, gwamnatin Buhari ta ce za ta sayar da NNPC idan aka yi wa Kudirin Dokar PIB kwaskwarima.

Rahoton ya ce idan NNPC na tafiya a haka, babu yadda za a yi lamurra su rika tafiya daidai kenan.

NNPC Group ya kunshi Hedikwatar NNPC, Sai kuma wasu bangarori 21, ciki har da NHC, NAPIMS, NPDC da NETC Limited da sauran su.

Tuni dai Shugaban Hukumar NNPC Mele Kyari da Gwamnatin Tarayya su ka fara fito da tsare-tsaren yadda za a ceto NNPC daga durkushewar da ba zai iya rike kan sa ba.

Share.

game da Author