Hukumar Hana Safara da Tu’ammali da Muggan Kwayoyi (NDLEA), ta bada sanarwar damke wani tsohon ma’aikacin ta da ta kora dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 253.
Korarren ma’aikacin mai suna Pam Ekekiel Adamu, an kama shi ne a garin Mokwa, cikin Jihar Neja, kamar yadda Babban Kwamandan Riko na Jihar Neja, Aloye Oludare ya shaida wa manema labarai.
Ya ce kafin a kore shi, Pam ya na da lambar dauka aiki ta SN. 5454, kuma ya yi aiki ne a Gombe. A cikin 2019 aka kore shi daga aikin NDLEA.
“Sun loda wa wata mota wannan tulin wiwi a garin Ado Ekiti, shi da wani da ake zargin su tare. Amma shi wancan dayan ya tsere, a kan hanyar su ta zuwa Adamawa.”
Shugaban na NDLEA ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu, da zarar an kammala bincike.
Ya roki jama’a su rika kai rahoton duk wani batagarin da ba su amince da shi ba.
“Mu na ta kokari mu na hada kai da sarakunan gargajiya da shugabanni da malaman addinai su rika kiran jama’a su na sanar da su kai rahoton duk wanda aka ga ya na safarar ko hada-hadar mugguman Kwayoyi.”. Inji shi.
Discussion about this post