Shugaban Kungiyar Manoman Najeriya (AFAN), Kabir Ibrahim, ya yi ikirarin cewa Ministan Harkokin Gona Sabo Nanono da wani mamba na AFAN mai suna Farouk Mudi, sun hada gidogar damfarar manoma, ta hanyar aikawa da wasiku cewa su sayi wasu kayan noma da aka yi wa rangwamen farashi, kuma ta asusun bankin Heritage Bank za su biya kudaden.
Ibrahim ya fitar da wannan bayani a ranar Talata.
“Mun gano cewa Ministan Harkokin Noma Sabo Nanono da Farouk Rabiu Mudi sun shirya wata gidogar damfarar manoma.
“Sun aika wasiku cewa a sayi wasu kayan noman, wadanda su ka ce an yi masu rangwamen farashi, kuma su biya kudaden ta asusun ajiyar Kungiyar AFAN mai lamba: 5100311797 da ke a Bankin Heritage.
“Mu na sanar da jama’a cewa su yi kaffa-kaffa, domin asusun ajiyar na harkalla ne aka bude da sunan Kungiyar Manoma ta Najeriya. Shi ya sa ma aka je can wani bankin da ba shi da wani nasibi aka bude asusun a can.”
Shugaban AFAN ya ce kayayyakin da Minista Nanono zai kaddamar tare da wasu Ministoci uku, ba su da inganci, kuma ba nagari ba ne.
“Kayayyakin fa ba su da inganci, sun dade a jibge, a ajiye a Keffi da Mando, tun cikin 2017.
“Idan kun tuna, a cikin 2019 an nemi mu je mu sayi kayan, amma babu wanda ya kula su, saboda kayan ba masu inganci ba ne, kuma an tsawwala masu kudi.
“An zabge wa kayan farashi kashi 76% kuma aka kwashi wasu aka bai wa Farouk Mudi da abokan kulla gidogar sa kyauta. Su ne kuma ya shirya walls-wallen sayar da su ga masu rabon dibga asara.”
Ya yi barazanar maka Minista da Ma’aikatar Gona kotu, ya na mai cewa dama harkalla ta zame wa Ma’aikatar jiki, domin yanzu haka Hukumar ICPC na sa mata ido akan wata cuwa-cuwar naira bilyan 16.
An tuntubi Kakakin Yada Labarai na Ma’aikatar Gona, Theodore Ogaziechi, ya ce shi ma a soshiyal midiya ya ga wasikar. Minista Nanono kuma ba ya nan ballantana ya ji daga bakin sa.
Discussion about this post