HARƘALLAR KUƊIN FANSHO: Rashin Maina da Mai Shari’a ya tsaida zaman kotu a ranar Litinin

0

Rashin Mai Shari’a Abang da wanda EFCC ta gurfanar, Abdulrashid Maina, ya tsaida shari’ar da ake zargin Maina da laifukan zamba 12, ciki har da zargin karkatar da naira bilyan 100.

A zaman Litinin a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, Mai Shari’a bai zauna ba, shi ma Maina ko sama ko kasa, kamar dai yadda ta faru a ranar 25 Ga Satumba da kuma 2 Ga Oktoba.

Sai dai kuma wanda ya karbe shi beli, wato Sanata Ali Ndume, ya kai kan sa kotun.

Ganin an dauki tsawon lokaci alkalin kotun bai halarta ba, sai magatakardan alkali ya sanar cewa , “duk wata shari’a ta manyan laifuka an dage ta sai washegari Talata.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Ndume a ranar Juma’a da ta gabata ya shaida wa kotu cewa ya nemi Maina na rasa, bayan na karbi belin sa -Inji Sanata Ndume a kotu.

Sanata Ali Ndume ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya a Abuja cewa, ya nemi tsohon Shugaban Kwamitin Kwatar Kudaden Fansho, Abdulrashid Maina, amma ya rasa inda ya ke.

Ndume ya yi wannan bayinin a matsayin sa na wanda ya tsaya a kotu ya karbi belin Maina, bayan ya shafe watanni bakwai a kurkuku saboda ya rasa mai beli.

An zargi Maina da karkatar da naira bilyan 100 na kudaden fansho. Sannan kuma ana zargin sa da laifin karkatar da kudade ta bahaguwar hanya, wato money laundering.’

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya, inda ta tuhume shi da aikata laifuka 13, ciki har da bude asusun ajiyar kidade na harkalla da kuma aika ayyukan zamba.

Jami’an SSS ne su ka damke shi cikin 2019, bayan ya shafe shekara daya cur ya na wasan-buya da jamii tsaro.

SSS sun damka shi a hannun EFCC, su kuma su ka gurfanar da shi kotu.

PREMIUM TIMES ta buga albarin yadda Sanata Ndume ya amince ya karbi belin Maina, bayan ya shafe watanni a tsaye, ya rasa mai belin sa.

Kotu: Yayin da Mai Shari’a ya nemi jin ta bakin Ndume, saboda a cikin sati sau uku ana umartar sa ya gabatar da Maina a kotu, amma abin ya gagara, Ndume a wannan karo ya ce ya nemi Maina sama ko kasa, amma ya rasa inda ya ke.

Tun da farko Mai Shari’a Abang Okon ya nemi Ndume ya kai Maina kotu a matsayin musayar kudin belin da ya ajiye.

Da farko an nemi sai an ajiye naira bilyan daya za a bayar da belin Maina, sai kuma mutum daya mai tsaya masa.

Daga baya saboda an rasa mai beli, alkali ya amince a ajiye takardun kadarorin da suka kai naira milyan 500 a Abuja, wanda Ndume ya bayar din aka ba shi belin Maina.

Ran Mai Shari’a ya baci matuka, inda a karshe ya ce tilas a ranar 5 Ga Oktoba, Ndume ya kai Maina a kotu, ko ana ha-maza-ha-mata.

Share.

game da Author