Haba Injiniya Buba Galadima, Adawa Fa Ba Hauka Ba Ce, Yanzu ‘Yan Arewar Ne Shashashu!? Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

‘Yan uwana masu girma, Allah Ta’ala yana fada a cikin littafinsa mai tsarki, wato Alkur’ani, yana cewa:

“Ku kiyayi, kuma kuji tsoron wata irin fitina wadda idan ta faru ba zata tsaya kawai akan wadanda suka jawo ta ba (zata shafi kowa da kowa), ku sani, lallai Allah mai tsananin ukuba ne.” [Suratul Anfal: 25]

Duba da ire-iren wadannan ayoyi na Alkur’ani Mai girma, da Hadisan Manzon Allah (SAW) masu tarin yawa da suke hana tayar da fitina a cikin kasa ko gari, yasa malaman addini suka tashi tsaye domin sauke nauyin da Allah Ta’ala ya dora masu, na kokarin hana ‘yan arewa da dukkanin ‘yan Najeriya masu saurarensu shiga wannan fitina da ta taso ta #EndSars. Domin kamar yadda muka sani, ita fitina abu ce da ba ta da amfani. Idan fitina ta afku babu wani abu da zai rage, kuma kowa sai ya dandani kudarsa. Idan ana cikin halin yaki, babu abun da zai yi tasiri. Idan Najeriya ta tarwatse babu abun da zai rage. Shi yasa duk wani mutum mai hankali, mai kishin kasar sa da al’ummarsa ba zai taba yarda da tashin hankali ko tarzoma ba da sunan zanga-zanga.

Sanadiyar kiraye-kirayen da malamai suka yi, suka gaya wa al’ummarsu, mutanen Najeriya da ‘yan arewa baki daya gaskiya, cewa kar su yarda su shiga cikin tayar da hankali da fitina, domin kowa ya ga irin abubuwan da ke faruwa na tashin hankali da zubar da jinin bayin Allah, da kone masu dukiya, da sace masu dukiyoyi, a wurare daban-daban da ake yin wannan zanga-zanga ta sharri. Shine kwatsam, sai wannan mutum, mai suna Injiniya Buba Galadima, da sunan adawar siyasa, ya kira ‘yan arewa shashashu, don kawai sun ki yarda su tayar da fitina.

Wallahi na karanta, kamar yadda shahararriyar jaridar nan ta yanar gizo, wato Premium Times Hausa ta wallafa, kuma na saurara da kyau, a wata hira da yayi da sashen Hausa na BBC, inda Injiniya Buba Galadima da sunan adawar siyasa, yake bayyana cewa ‘yan arewa shashashu ne har da suke kasa kunne suna sauraren malaman addininsu su na gaya masu cewa zanga-zangar kawo karshen rundunar tsaro ta #EndSARS, zanga-zanga ce ta kabilanci da banbancin addini. Yace shi da kansa ya ga masu yin wannan zanga-zangar ta #EndSARS suna tattakin su cikin kwanciyar hankali da natsuwa, suna tafiya a gefen titi a Abuja. Yace wai ko titi ba su hawa saboda natsuwa da kamala, amma kuma sai ga wasu wai da ake zato daga wasu jihohi aka kawo su sun tarwatsu su (yana nufin kenan an yi hayar matasan arewa sun tarwatsa su). Yace ire-iren kiraye-kirayen da malaman addini suka rika yi na cewa ‘yan arewa su kaurace wa zanga-zangar, tare da yi masu huduba a masallatai, suna cewa akwai wata makarkashiya da wani shiri na daban a cikin ta bai dace ba. Yace dole ne ‘yan arewa su daina nuna kiyayya ga ‘yan kudu, saboda idan ba haka ba idan suka samu kujerar shugabancin Najeriya zasu iya ciwa arewa da ‘yan arewa mutunci su ma.

Haba Buba Galadima yanzu ‘yan arewar ne kake kira shashashu? A gaskiya sai yanzu na kara fahimtar ko kai wanene! Kuma sai yanzu na kara gano manufarka. Ashe duk ihu da babatun da kake yi da sunan adawar siyasa, ashe kai so kake yi ka tunzura ‘yan arewa suyi tashin hankali, suyi kone-kone, su kashe junansu, su kara jefa yankin cikin matsala ko!

Yanzu don Allah kalli irin halin da jihar Legas da sauran wuraren da ake yin wannan zanga-zanga suka sami kansu a ciki sanadiyar wannan tarzoma marar amfani. A inda aka yi asarar rayuka da dimbin dukiyoyi.

Yanzu don Allah zaka iya gamsar da mu irin abun da ake so a cimmawa na alkhairi da wannan zanga-zangar? Yanzu don Allah wadannan masu wannan tarzomar sune kake so ‘yan arewa su biye ma wa, su fito suyi kone-kone da tayar da hankalin jama’ah? Saboda basu yi ba shine kake kiransu shashashu?

To ‘yan arewa, yanzu kun dai ji, kuma kun kara gane waye Injiniya Buba Galadima. Idan alkhairi yake nufin ku da shi zaku gane, idan kuma akasin haka ne yake nufi zaku gane.

Wallahi ya zama wajibi ku hankalta, kuma ku kiyayi shiga duk wani abun da baku san asalinsa, ko dalilinsa ba. Kuma ina kara rokon Allah da ya saka wa matasan arewa da Alkhairi. Domin sun fitar da mu kunya, kuma sun nuna cewa su ‘yan halal ne, masoya Najeriya ne; kuma sun nuna cewa su masu da’a da tarbiya ne, ba shashashu ba ne kamar yadda wannan mutum Injiniya Buba Galadima yake fada.

Kuma ina kara kira ga ‘yan uwana ‘yan arewa cewa, wallahi kar ku yarda wasu mutane suyi amfani da ku wurin tarwatsa garuruwanku da sunan zanga-zanga!

Su wadancan iyayen gidan naku, turawan yamma, wadanda kuka dauko siyasar dimokradiyya hannun su, ai ba haka suke yin tasu dimokradiyyar ba. Duk banbancin da ke tsakaninsu na jam’iyyah, za ka tarar manufarsu daya ce; ita ce ciyar da kasar su da kuma al’ummarsu gaba, tare da tunkude sharri daga gare su, da kawo masu ci gaba. Ba zaka samu wani dan siyasa a Amerika ko Ingila ko Faransa yana kokarin tunzura jama’ar kasa, ko matasa, suyi tashin hankali ko tayar da fitina, da sunan adawar siyasa ko zanga-zanga ba. Irin wannan mummunar dabi’a sai a wurin ‘yan siyasar afrika. Anan ne zaka tarar da dan wata jam’iyyah yana kokarin kawo matsala, don ace abokin adawar sa ya gaza, sai yayi murna, yaji dadi.

Irin wannan mummunar adawa da sunan siyasa, wallahi ba ya da kyau, kuma sam bai dace ba. Irin shi ne yake faruwa a jiha ta ta Zamfara. Inda tsohon gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari, shi da magoya bayansa, kullun kokarin su shine, su ga gwamna mai ci yanzu, Muhammad Bello Matawalle ya kasa, sai su ji dadi, suyi masa dariya, kuma wai duk da sunan adawar siyasa. Shi gwamna Bello Matawalle, duk duniya ta shaida, ko hasidin-iza-hasada ya san da cewa yana iyakar kokarinsa wurin ganin an kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi jihar Zamfara. Amma sai aka wayi gari da sunan adawar siyasa, da sunan banbancin jam’iyyu na APC da PDP, tsohon gwamna da magoya bayansa, suna kokarin kawo masa cikas da sunan adawar siyasa. A duk lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari a jihar Zamfara, suka kashe mutane, zaka tarar da duk jihar ana jimami, ana zaman makoki, an shiga damuwa tare da gwamna Matawalle. Amma shi tsohon gwamna da magoya bayan sa wallahi murna suke yi, suna jin dadi, wai an kai hari, an kashe bayin Allah. Kuma duk suna yin wannan ne saboda ace gwamna ya kasa. Wai kuma duk wannan, da sunan adawar siyasa.

Haka nan ma gwmanan jihar Borno, Farfesa Zulum, yake fuskantar irin wadannan matsaloli. Shi yana kokarin ganin cewa an kawo karshen matsalar tsaro ta Boko Haram da ta addabi jihar, amma wasu miyagun mutane suna ta yi masa zagon-kasa da sunan adawar siyasa.

Wadannan fa sune kadan daga cikin halayen mu da dabi’un mu. Da sunan adawar siyasa muyi ta jefa al’ummomin mu cikin matsala. Alhali su turawa, wadanda suke sune iyayen dimokradiyyar basu yin haka.

To irin wannan shine Injiniya Buba Galadima da matar nan mai suna Aisha Yusufu suke yi. Suna ta tunzura matasa, musamman na arewa, da su fito domin su tayar da fitina. To ganin cewa malaman addini basu yarda da wannan mummunan ra’ayi nasu ba, kuma malaman suna ta kiraye-kirayen matasa da ka da su shiga wannan zanga-zanga, kuma matasan sun amsa kiran malaman, shine sai aka wayi gari Buba Galadima da Aisha Yusufu da ire-iren su suke jin haushin malaman, suke cin mutuncin su, kuma suna kiran ‘yan arewa shashashu.

Alhali sun manta da cewa mutanen arewa mutane ne masu da’a da tarbiyya da biyayya, kuma mutane ne masu kokarin kamanta bin addinansu.

Yanzu don Allah asarar da masu wannan zanga-zanga suka jawo a wuraren da ake yin ta waya san iyakar ta? Don Allah Buba Galadima ka san iyakar ‘yan arewa da aka kashe kuma aka sace, tare da kona masu dukiyoyi, a Fatakwal, da Edo, da Legas, da Aba da sauran wurare da sunan wannan zanga-zangar? Yanzu don Allah ban cin da malaman addini suka tashi tsaye, suka kira mabiyansu, da suyi hakuri, kar suyi wannan zanga-zangar a arewa, kuma suka amince, da ka san irin ta’adin da za’a yi? Domin da ace mutanen arewar da ka kira shashashu sun mayar da martani, domin yin ramuwar abun da aka yiwa ‘yan uwansu a kudu da zaka zauna Najeriyar? Haba Injiniya Buba Galadima, wai me yasa ne hankalin ku yake gushewa da sunan adawar siyasa? Ya kamata fa muji tsoron Allah, kuma mu tuna da cewa akwai mutuwa kuma akwai hisabi!

Ai ko su wadanda suka bayar da kudadensu domin goyon bayan wannan fitinar da sunan zanga-zanga, ga shi nan abun yafi karfinsu, abun ya zamar masu kaikayi-koma-kan-mashekiya. Sun shirya abun domin cimma wata manufa ta siyasa tare da rusa arewa, amma gashi nan abun ya koma kan su. Dama ance, MUNAFUNCI DODO NE MAI SHI YAKE CI! Gobe ma su sake shirya irin wannan bala’i, zai sake komawa kan su da yardar Allah!

Saboda haka, Injiniya Buba Galadima, Aisha Yusufu da ire-iren ku ina mai gargadinku da ku shiga taitayinku. Da ikon Allah mummunan halin da kuke so ku zuga mutanen arewa su shiga na yaki da tashin hankali, da tayar da tarzoma, Allah ba zai baku nasara ba. Wannan karon Allah ya kare arewa da jama’arta daga sharrinku, don haka alhamdulillahi, muna godiya ga Allah akan wannan.

Yanzu kai Injiniya Buba Galadima don Allah ‘ya ‘yan ka da suka yi karatu, daga mai digiri biyu sai mai digiri uku, wasu ma suna aiki, shin matasan arewa da kake zugawa suyi tashin hankali sun yi karatu irin na su, ko sun samu aikin yin? Ya kamata muji tsoron Allah mana!

Kuma ina so jama’ah su sani, duk wannan abu da ke faruwa, da bayanan da muke yiwa al’ummarmu, ba wai muna nufin cewa ‘yan arewa basu shan wahala a wannan gwamnatin ba ne, a’a. Ai kowa yasan cewa ‘yan arewa suna shan wahala matuka a wannan mulkin, kai su suka fi kowa ma shan wahala a wannan gwamnatin. Domin a shekaru shida na wannan gwamnatin in ban da rashin tsaro, yunwa, talauci, jahilci, rashin aikin yi, da rashin ababen more rayuwa, da rufe iyakar kasa (wato boarder), babu abunda ‘yan arewa suka karu da shi! Amma abun da muke kokarin cewa shine, ba zai yiwu ba, muna cikin wadancan musifun kuma a kara afka mu cikin wasu, abubuwa su kara cakude muna! Wannan shine kiraye-kirayen da muke yi.

Misali, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ai shi ma dan jam’iyyar adawa ne ta PDP, amma da yake yana kishin kasarsa da kuma al’ummarsa, ai kowa yaji firar da aka yi da shi a BBC Hausa. Yayi maganganu masu kyau, kuma masu dadi, na kwantar da hankalin jama’ah. Amma shi wannan Injiniya Buba Galadima, ba abun da yake yi sai zuga mutanen arewa da tunzurasu su ma su fito suyi tarzoma. Da suka ki sauraronsa shine ya zage su, ya kira su shashashu!

Allah yasa mu dace, yayi muna jagora.

Daga karshe, ina rokon Allah Ta’ala ya kare muna kasar mu Najeriya da arewar mu daga sharrin duk wasu masharranta, kuma ya zaunar da mu lafiya, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author