Gwamnatin Tarayya ta bada hujjar goranta wa ƴan Najeriya sayen fetur da arha

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa dora sikelin arhar litar man fetur din Najeriya da sauki fiye da kasashen Saudi Arabia da wasu kasahe, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a jawabin sa na ranar zagayowar samun ‘yanci, to daidai ne.

Ministan Harkokin Yada Labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da Gidan Radiyon FRCN na Kasa, cikin wani shiri mai suna “Radio Link”, ranar Asabar, a Abuja.

Shugaba Buhari ne ya nuna cewa ‘yan Najeriya na shan ferur arha tibis, naira 161, kasa da Saudi Arabia da ake saida lita daya daidai da naira 168.

“Masar na sayar da lita 1 naira 362, Nijar kuma naira 346. Sai Ghana naira 362.

“Ai sam ba abin yarda ba ne, domin bai yi daidai ba a ce ana saida litar fetur a kan farashi kasa da wadannan kasashe, kamar Saudi Arabia.” Inji Buhari.

Daga nan ‘yan Najeriya har zuwa yanzu su na ci gaba ragargazar Buhari, tare da nuna cewa albashin da ake biyan ma’aikatan Saudiyya a wata, ya nunka na Najeriya sau goma.

Sai kuma da ya ke amsa tambaya a kan wannan, Minista Lai cewa babu wani aibi don Buhari ya kwatanta irin farashin litar mai a Najeriya da kuma Saudiyya.

“Mu amsar da zan ba irin wadannan mutanen su ne Saudiyya mutum milyan 34 gaba dayan su. Najeriya kuma na da yawan mutum milyan 200.

“Saudi na hako gangar danyen mai milyan 10 a kullum, Najeriya kuma na hako milyan 2.1 a kullum.

“Yawan al’ummar Saudi Arabiya bai fi kashi daya bisa shida na yawan ‘yan Najeriya ba. Amma kuma su na da dimbin arzikin ferur fiye da Najeriya.

“Don haka za su iya biyan albashi mai yawa, kuma kudaden su za su wadace su yi wa al’umma ayyukan raya kasa masu tarin yawa.

“To mu na a dubi maganar da mu ke yi a wannan gabar. Mun ce duk kudaden rarar tallafin mai da aka soke biya, za a rika tattara su ne ana yi wa al’umma ayyukan bunkasa kasa da su.” Inji Lai.

Ya jinjina wa Kungiyar Kwadago ta Kasa, saboda janye fita zanga-zanga da fasa tafiya yajin aikin da su ka yi.

Ya ce da an barke da yin wannan yajin aiki, to da Najeriya ta afka cikin “bala’in da zai mamaye kasar nan baki daya.” Inji shi.

“Tskanin 2006 har zuwa 2019, Najeriya ta biya kudaden tallafin mai har naira tiriliyan 10.413. Duk shekara kusan naira bilyan 743.8 kenan. Amma a gaskiya daga yanzu Najeriya ba za ta iya jure ci gaba da yin wannan caca ko dibga asara ba.” Cewar Lai.

Share.

game da Author