Gwamnatin Najeriya na kan hanyar daƙile ta’addanci, ‘yan bindiga da mahara -Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada kokarin da ya ce gwamnatin Najeriya ke yi wajen kawo ƙarshen ƴan ta’adda, ƴan bindiga, mahara da masu garkuwa da mutane a ƙasar nan baki ɗaya.

Buhari ya jaddada wannan kalami a wurin taron yaje kananan sojojin da su ka kammala kwas na kwararru da wadanda su ka kammala kwas na gajeren zango, a makarantar horon sojoji ta NDA, Kaduna.

Wannan bikin dai an yaye daliban Kwas na 67 na Kwararru da kuma Kwas na 46 na Gajeren Zango a NDA din.

“Mu na nan kan hanyar tabbatar da cewa mun kakkabe ta’addanci, ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

“Mu na kuma kan kokarin ganin mun dakile duk wasu manya da kananan laifuka a kasar nan baki daya.

“Za mu dakile duk wani kalubalen da kasar nan ke fuskanta ta fannin tsaro.

“Wadannan zarata da aka yaye a yau, ina da yakinin cewa sun samu ingantaccen horo da kwarewa da juriyar fuskantar kalubalen da kasar nan ke fama da su.

“Saboda haka ina jan hankalin ku da jajircewa tare da nuna kishi da kaunar kasa da kuma dabbaka zaman lafiya da hadin kan kasar nan baki daya.”

Buhari ya kuma jinjina wa dakarun Najeriya wadanda ke tabbatar da tsaro da dakile ta’addanci a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

Buhari ya kara da cewa ya gamsu da irin kwakkwaran horon da NDA ke ba kananan hafsoshin sojojin kasar nan, wadanda ya ce ko kadan ba su jikarar tunkarar duk wani ko wata barazana ko kalubale ga tsaron kasar nan.

Ya kuma gode wa Kwamandan Horas da Hafsoshi na NDA.

Share.

game da Author