Gwamnatin Jihar Lagos ta ce za ta binciki yadda aka buɗe wa masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin ta ce za ta binciki yadda aka bude wuta har aka kashe wasu masu zanga-zanga, kuma aka raunata wasu da dama.
Wasu jami’an tsaro ne da aka tabbatar sojoji ne su ka bude wa masu zanga-zanga wuta a shingen karbar kudaden haraji a hannun masu ababen hawa, wato toll gate a Lekki.
Tsawon makonni biyu kenan ana ci gaba da zanga-zangar neman rushe ‘yan sandan SARS saboda cin zarafi da take hakkin jama’a da su ke yi, musamman kisan wadanda ba su ji ba, kuma ba su gani ba.
Zanga-zanga ta yi muni sosai a ranar Talata a Lagos, inda aka yi kone-komen wasu ofisoshin ‘yan sanda da kuma arangama da ‘yan Sandan.
Hakan ya tilasta Gwamnam Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu kakaba dokar-ta-baci, inda aka hana zirga-zirga daga karfe 4 na yammacin Talata zuwa safiya.
Sai dai kuma masu zanga-zanga sun yi kunnen-uwar-shegu da dokar hana zirga-zirga, su ka rika taruwa su ka yi dandazo a Lekki daidai ‘toll gate.’
Wajen karfe 7 na dare kafin a fara harbin masu zanga-zanga, Gwamnatin Lagos ta sanar cewa dokar-ta-baci za ta fara aiki karfe 9 na dare, maimakon karfe 4 na yamma da aka yi sanarwa da farko.
Jami’an gwamnati sun cire CCTV kyamara din da ke wuraren, kuma aka kashe fitilun kan titi. Jim kadan kuma sai wasu da ake da yakinin sojoji ne su ka bude wa masu zanga-zangar wuta.
Gwamnatin Jihar Lagos ta tabbatar da an harbi masu zanga-zangar, kuma ta ce za ta yi bincike.
Da jijjifin safiyar Laraba kuma Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana cewa jami’an tsaron da su ka fi karfin karbar umarni daga gwamnatin sa ne su ka bude wa masu zanga-zanga wuta a Lekki.
Duk da haka dai ya ja hankalin jama’a tare da yin rokon cewa a kwantar da hankali kuma a daure a zauna a gida.