A wata sanarwa da ta fito daga ma’aikatar ilimin jihar Kaduna wanda Kwamishinan Ilimin jihar Shehu Muhammad ya saka wa hannu, makarantun Sakandaren jihar Kaduna za su koma karatu daga ranar 18 ga Oktoba.
Sanarwar ta bayyana cewa daliban ajujuwan SSII na babban sakandare da na JSSII ta karamar Sakandare za su koma karatu daga ranar 18 ga watan Oktoba.
Bayan haka kuma za a rika yin karatun safe da yamma ne yanzu.
Wasu za su zo da safe wasu kuma da yamma.
Za a rika zuwa da safe karfe 8 – 12 na rana da kuma karfe 1 zuwa 5 na yamma.
Sannan kuma kada a wuce mutum 20 a kowanne aji, kuma a tabbata an ba da tazarar mita 1.5 tsakanin kujerar kowanne dalibi.
Kowacce makaranta sai ta kafa kwamitin kiyaye dokar Korona wanda za su rika bi suna duba yadda dalibai ke kiyaye wa da malaman su. Wannan kwamiti zai hada harda mambobin kungiyar iyaye na makarantar, jami’an kiwon lafiya da na unguwar da makaranta take.
Iyaye za su samar wa ‘ya’yan su takunkumin fuska da kuma man tsaftace hannaye idan za su zo makaranta.
Dole sai makarantu masu zaman kansu sun yi rajistar amincewa da bin dokokin korona daga hukumar kula da makarantu ta jihar kafin su bude makaranta.
Haka kuma makarantun Islamiya suma sai sun samu wannan takardar shaidar amincewa daga hukumar kula da makarantun jihar kafin su bude makarantu.
Bayan haka gwamnati ta ce har yanzu za a cigaba da samar da karatu ta yanar gizo, radiyo da talbijin kamar yadda ake yi a baya.
Gwamnatin Kaduna ta ce za ta sanar da ranakun komawar sauran ajujuwan nan ba da dadewa ba da suka hada har da makarantun Firamare.