Gwamnati za ta rika mu’amala da matasan kasar nan da gaskiya da amana – Osinbajo

0

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya ce duk wata hulda da za a yi da matasa, kada ta zama akwai nuku-nuku ko yaudara. Ta kasance keke-da-keke ce cikin gaskiya da amana.

Osinbajo ya yi wanann bayani a lokacin da ya ke karbar bakuncin Kwamitin Shugabannin Majalisar Matasa ta Najeriya, karkashin jagorancin Simon Elisha, a ranar Talata.

Kakakin Yada Labarai na Mataimakin Shugaban Kasa, Laolu Akande ne ya sanar da wannan ziyara cikin wata sanarwar da ya fitar ga manema labarai.

Mataimakin Shugaban Kasa ya ce Shirin Inganta Rayuwar Jama’a (SIPs) ba an bijiro da shi ba ne ta hanyar bai wa ma’aikatan gwamnati da ‘yan siyasa guraben daukar makusantan su.

Ya ce an kirkiro shirin yadda ‘yan Najeriya wadanda ba su san kowa ba, kuma ba su iya neman kamun-kafa ko alfarma za su ci moriyar sa, su amfana.

“Matsalar farko da aka fara fuskanta ita ce kowa na so a ba shi guraben da zai kawo sunayen wadanda ya ke so a dauka. Ni kuma na ce ba zan yi hakan ba. Saboda me? Saboda idan na yi haka, to na lalata shirin gaba daya. Domin mafi yawan ‘yan Najeriya ba su san wanda za su yi kamun-kafa da shi ba, ko su nemi alfar ma a gare su.

“Ban ce wai ni ma’asumi ba ne ba na kuskure. To amma dai matsawar matasan mu ba za su iya samun aiki ko wasu gurabe ba, sai sun san wani a sama, to a gaskiya mun ci amanar su.

“Wata rana Shugaba Buhari ya kira ni, ya ce min, “ga shi yanzu-yanzu ina sauraren BBC Hausa, wasu matasa biyu ana hira da su, sun ce ba su san kowa ba, amma su na cin moriyar naira 30,000 ta N-Power kowanen su a duk wata. Buhari ya ce min hakan na nuni da cewa kwalliyar mu na biyan kudin sabulu kenan.”

Osinbajo ya kara da cewa shi ya sa a lokacin kamfe na zaben 2019, duk inda su ke je za a ga irin wadanda su ka ci moriya daban-daban, sun kafa kungiyoyin goyon bayan su.

Sauran mambobin da su ka raka Simon ziyara ga Osinbajo, sun hada da Hafiz Kawu Tarauni, Kabiru Tukura da Saidu Abdulalhi.

Share.

game da Author