Majalisar Zartaswa ta amince da kashe naira bilyan 1.6 wajen bude Shafin Tantance Sahihancin Kwangiloli a intanet, domin magance almundahana, aringizo da harkallar da manyan jami’an gwamnati ke yi wajen bada Kwangiloli.
A zaman Majalisar Zartaswa na ranar Laraba karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari aka amince da wannan tsari domin dakile satar makudan kudade ta hanyar kwangiloli.
Shugaban Hukumar Tantance Kwangiloli Mamman Ahmadu ya ce tsarin zai yi matukar amfani wajen hana almundahana, kuma zai gyara tsarin bayar da kwangiloli.
Ya ce hukumar BPE da ya ke shugabanci ce ta gabatar wa Gwamnatin Tarayya da wannan dabarar bude shafin, kuma ta amince.
Baya ga rage almundahana da zamba a tsarin kwangiloli, tsarin mai suna ‘E-Government’ zai kuma kawo sauki da saurin tantance kwangila da saurin amincewa da ita, “ba kamar yanzu da ake daukar lokaci kafin a tantance, a amince ba, har jama’a da dama na korafin daukar lokacin da ake yi.” Inji Shugaban BPE.