Gwamnati jihar Filato ta kafa kotuna guda bakwai domin yin shari’a da hukunta barayin abincin tallafin korona 307 din da aka kama a jihar.
Gwamnati ta fadi haka ne bayan an tashi taron tattauna matsalolin sace–sacen kayan abinci da wasu ‘yan isakan gari suka yi a jihar kwanaki biyu da suka wuce.
Da yake ganawa da manema labarai a fadar gwamnati dake Rayfield Jos sakataren gwamnatin jihar, Danladi Atu ya ce gwamnati ta kafa wadannan kotuna ne a wuraren da aka sace kayan abincin a jihar.
“Zuwa yanzu komai ya lafa sai dai akwai alamun wasu ‘yan isakan gari za na shirin sake far wa shagunan mutanen da wasu wuraren ajiya kayan abinci na gwamnati.
Gwamnati ta Kuma amince ta kakkafa shingayen tsaro a kananan hukimomin Jos ta Kudu da Jos ta Arewa domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Atu ya ce gwamnati ta umurci jami’an tsaro a jihar da su cigaba da farautar wadanda suka saci kayan abincin domin yanke musu hukunci.
Ya gargaddi mutane da kada su ci kayan abinci da suka sata saboda an zuba maganin kwari a ciki domin hana abincin lalacewa da wuri.
Gwamnati ta jinjina kokarin da jami’an tsaro suka yi wajen samar da tsaro a jihar tun kafin lalacewar ya fi haka.
Sannan gwamnati ta ce za ta yi kokari wajen biyan bukatun jami’an tsaron domin karfafa musu gwiwa wajen gudanar da aiyukkan su a jihar.
Wuraren da ‘yan isakan gari suka saci kayan abinci a jihar.
Daya ranar 26 ga Oktoba ‘yan isakan gari sun saci Kaya a dakin ajiyan Kaya na hukumar bada again gaggawa ta jihar SEMA dake Old Nitel Bukuru, PRUWASSA, PADP dake Dogon Dutse, a garin Jos, ma’adanar kauan albarkun duwatsu ta ƙasa dake Angul D Bukuru, ASTC Vom, Kamfanin bugs takardu na jihar Filato, SUBEB dake dogon Dutse, kwalejin koyar da fasaha na gwamnati Bukuru, hedikwatan karamar hukumar Ryom, makarantar koyar da kirke-girke da dabarun kula da gida dake Vom, Kamfanin Jos Foods, filin baje kolin Jos da gidan tsohon kakakin majalisar dokoki ta ƙasa Yakubu Dogara.
Daga nan sai Kamfanin Grand Cereals Bukuru, ofisoshin gwamnatin jiha da gwamnati tarayyar da wasu gidajen mutane.