Watanni shida kacal bayan Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kori Kwamishinan Ayyuka, Muaz Magaji, saboda murnar mutuwar Abba Kyari da ya yi, yanzu kuma ya sake nada shi kan wani mukami daban.
Magaji ya shiga shafin sa na Twitter ya nuna murnar mutuwar tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaba Muhammadu Buhari, Kyari.
Wannan zafafan kalamai sun tashi hayaniya a kasar nan, har Ganduje ya gaggauta tsige shi.
Ba Magaji ne kadai cikin hadiman Ganduje ya taba caccakar gwamnatin Buhari ba. Farkon wannan wata ne Ganduje ya dakatar da hadimin yada labaran sa, Salihu Tanko Yakasai, saboda shi ma ya shiga Twitter ya nuna cewa Buhari ba shi tausayi, saboda ya ki maida hankali kan masu zanga-zangar #EndSARS.
A yau kuma sai ga sanarwa daga Kakakin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Uba Abdullahi, inda ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Ganduje ya nada Magaji shugabancin kwamitin kula da masana’antu na Jihar Kano.
PREMIUM TIMES ta buga labarin katobarar da Magaji ya yi a lokacin ya na Kwamishinan Ayyuka na Ganduje, inda ya nuna mutuwar Kyari wani alakakai ne Allah ya raba Najeriya da shi.
Ana mamakin yadda Ganduje ya maida Magaji cikin gwamnatin sa, duk kuwa da abin da ake gani kamar cin-fuska ne ya yi wa Buhari da kuma gawar Kyari ita kan ta.
Sannan an fara tunanin irin biyayyar da Ganduje ke wa Buhari, ganin yadda Salihu Yakasai ya sake dagargazar Buhari shi kan, ba ma gwamnatin sa ba. Amma dai da dama na ganin beken Ganduje da ya sauke Yakasai kawai, maimakon ya tsige shi.
Dawo da Magaji cikin gwamnatin Ganduje, da dama na ganin kamar shi ma Ganduje din jinin Buhariyya ya rage gudana a cikin jikin sa.