Fafaroma Francis ya nuna goyon bayansa ga aure da tarayya tsakanin jinsi daya

0

Shugaban mabiya Darikar Katolika Pope Francis, ya goyi bayan auren jinsi daya, wato namiji da namiji, mace da mace.

Papa Roma Francis ya fadi haka ne a wani fim mai taken ‘Francesco’ da wani fitaccen mai hada fina-finai daga kasar Rasha Evgeny Afineevsky ya hada.

Fafaroma yace suma irin wadannan mutane Allah ne ya yi su saboda haka suma suna da ‘yancin zabin abinda suke so su yi da rayuwar su. Ya Kamata ne a yi dokar da zai kare su da mutuncin su.

Kafar yada labarai mallakin cocin Katolika ta bada labarin wanda gidan jaridar CNN ya wallafa.

Bayan haka kuma Fafarom ya tofa albarkacin bakinsa kan matsolin canjin yanayi, tattalin arziki kashen duniya ke fama da su da sauran su.

Za a Fara nuna wannan fim a kasar Roma ranar Laraba.

Sannan a nuna fim a yankin Arewacin Amurka ranar Lahadi.

BBC ta rawaito cewa tun Fafaroma na shugabanin cocin Buenos Aires a Argentina yake da ra’yin mara wa masu ra’ayin jinsi daya baya a barsu su rika rayuwarsu kamar kowa.

Korafin mutane

Mutane da dama yan darikar Katolika basu amince da wannan matsayi na fafaroma ba. Sunce fada da mara wa masu irin wannan manufa baya sabo ne a addinance.

Sun ce ra’ayoyin Pope Francis gau auren jinsi daya sun yi hannun riga da ra’ayin tsohon Fafarom Benedict XVI.

A kasashen Afrika da Najeriya sam basu amince da haka ba domin akwai tsauraran matakai da aka saka domin hukunta duk wanda aka samu yana da alaka da abu irin haka wato auren jinsi daya.

Share.

game da Author