Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa Gwamnati za dauki matakan fara sauya wa tsarin aikin dan sanda fasali ta hanyar yi wa rundunar ta kasa baki daya garambawul.
Osinbajo ya yi wannan bayani ne a matsayin sako ga matasan da ke zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS.
Da ya ke magana a Fadar Shugaban Kasa, Osinbajo ya amsa wata tambaya ce da manema labarai su ka yi masa.
An tambaye shi ko wane sako ya ke da shi ga matasan da ke ci gaba da zanga-zanga, duk kuwa da an rushe SARS tun a ranar Lahadi.
“Ina ganin tuni mun rigaya mun dauki matakin sauya wa aikin dan sanda fasali ta hanyar rushe SARS. Abin da kuma zai biyo baya a yanzu shi ne kafa binciken wadanda su ka aikata laifukan danne hakkin jama’a a cikin su, a hukunta su.
“Daga nan kuma sai kafa wadanda za su maye gurbin su, wadanda za su yi aiki bisa abin da tsarin mulki da dokar kasa ta tanadar, ba tare da tauye hakkin al’umma ba.
“Saboda ba na jin wani ya fi wani damuwa da korafe-korafen da ake yi a kan take hakkin jama’a da SARS ke yi.
Ni kai na shaida ne, na sha samun bayanan zargin take hakkin matasa da su ke yi, ana neman na sa baki.” Inji Osinbajo.
Ya kuma kara da cewa, shi kan sa Sufeto Janar na ‘yan sanda ba kokarin ganin an shigo da farar hula, musamman kungiyoyi na kare hakkin hakkin jama’a wajen garambawul din da za a yi wa aikin ‘yan sanda, yadda za a guji take hakkin jama’a.
Ya kuma bada misali da bayanin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a kan garambawul din da za a yi wa harkar ‘yan sanda baki daya.