#EndSARS: Za a fara horas da sabbin ‘yan sandan SWAT, duk da zanga-zangar rashin amincewa da ke gudana

0

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammad Adamu ya bayyana cewa sabbin ‘yan sandan musamman da za su maye gurbin SARS, za su fara karbar horo a ranar Litinin din nan.

An dai rusa SARS, aka maye gurbin su da SWAT.

Sai dai kuma runi ‘yan Najeriya su ka yi fatali da wannan sabon suna, su na cewa ai da SARS da SWAT duk Danjuma ne da Danjummai.

SARS, wadda ke nufin ‘Special Anti-Robbery Squard’, an maye gurbin su da SWAT, wato ‘Special Weapons And Tactics’ Kakakin Yada Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Frank Mba, ya shaida cewa sabbin zaratan za su rika aiki ne a cikin nuna kwarewa, ka’idar doka da oda, bin tafarkin hakkin dan Adam da kuma bisa tsarin da ka’idar kasashen duniya su ka zartas da amincewa.

Ya an shirya irin horo da horaswar da za a yi wa sabbin jami’an SWAT tare da Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC) da wasu kungiyoyin bunkasa rayuwar al’umma da dama.

Sufeto Janar Adamu ya ce za a horas da su ne a Makarantar Horas da ‘Mobile Police’ ta Oragun, a Jihar Osun da kuma ta kan Tsaunin Ende, Jihar Nasarawa.

Ya kuma kara jaddada cewa ba za a dauki ko da wani jami’in dan sanda daya tal da ya taba aiki a karkashin SARS ba.

“Wadanda aka dauka matasan ‘yan sanda ne, zarata, wayayyu, gogaggu kuma masu jini a jika. Kuma dukkan su sun kai akalla shekaru bakwai zuws sama, su na aikin dan sanda kuma ba a taba kama kowanen su da aikata laifi ba.

“Babu wanda aka taba kamawa da laifin take hakkin jama’a ko amfani da bindiga ba bisa yadda doka ta ce ba.

“Za a masu aune-aune da gwaje-gwaje. Duk wanda aka ga bai cancanta ba, za a ce kawai ya koma cikin game-garin ‘yan sanda ya ci gaba da aikin sa.” Inji Adamu

A karshe ya roki ‘yan Najeriya su kara hakuri, kuma za a samu nasarar dakile laifuka a karkashin SWAT, ba tare da take hakkin jama’a ba..

Share.

game da Author