Duk da kira da shugaban kasa yayi na matasa su janye daga titunan Najeriya musamman jihohin kudancin Najeriya, har yanzu matasan basu bi wannan umarni ba domin sun ci gaba da farfasa shaguna da gidaje suna sace-sace a wasu jihohin kasar nan.
A jihohin Oyo, Ekiti, Legas, Osun, har yuanzu ‘yan iska na cigaba da cinnawa gidajen sanatoci, manyan jihohin da ofisoshin gwamnati wuta sannan suna sace-sace a gidaje da shagunan mutane.
Wadannan matasa kuma batagari sun afka gidan Sanatan dake wakiltar Oyo ta Tsakiya, Teslim Folarin, inda suka kwashe kayan tallafi da ya siyo domin mutanen gundumar sa.
Jihar Kwara
Matasa sun afka wa ofishin rundunar Kwastam dauke da bindigogi, adduna, da layu a jikunna su.
Kuk da cewa shugaban ofishin Kwastam nid ya yi kokarin kwantar musu da hankali abin ya citura, daga akarshe dai sai da aka yi batakashi da matasan, sai da suka kayi musayan wuta a tsakanin su.
Shugaban kwastam din ya ce an ji wa jami’ai biyu ciyu a arangamar. Yanzu suna asibiti ana duba su.
Jihar Koross Ribas
A jihar Koros Ribas, kuma masu zanga-zanga sun afka wa ofishoshin kungiyar Kwadago na jihar, ofishin hukumar Zabe da na bada agajin gaggawa ta jihar.
A nan ma sun sace kayan aiki da duk wani abin amfani da suka iske a ofisoshin.
A dalilin haka jihar Ekiti ta sake saka dokar ta baci a jihar.